Mai martaba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya kaddamar da wasu muhimman ayyuka na gyare-gyare a fadar Nasarawa, a yayin da ake kan ganiyar rikicin masarautar Kano.
Bayero dai yana zaune ne a karamar fadar Nasarawa tun bayan tsige shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a farkon wannan shekarar, wanda ya mayar da Sarki Sanusi II kan karagar mulki.
Tunanin kwaskwarimar ga fadar ya haifar da cece-ku-ce inda hakan ke nuni da aniyar sarki Bayero na ci gaba da da’awar Sarauta duk da cewa, gwamnatin jihar tuni ta tsige shi.
Dan mori na Kano, Abubakar Hassan, wanda kuma mai biyayya ne ga Sarki Aminu Bayero, ya tabbatar wa manema labarai fara kwaskwarimar ga karamar fadar. “Sarki ya fara fadada Hubbare, wacce aka fi sani da makabartar tsoffin Sarakunan Kano, kamar marigayi Sarki Abbas, ina iya tabbatar da cewa, tuni an fara aiki daga cikin gidan sarautar,” in ji Hassan.