Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya bayyana a bainar jama’a a karon farko a ranar Asabar din da ta gabata, tun bayan fara rikicin masarautar Kano biyo bayan tsige shi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.
Sarki Aminu ya halarci wani taro ne, wanda shi ne babban taron karatun saukar Alkur’ani mai tsarki da iyalan marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi’u suke gudanarwa duk shekara.
- Binciken CGTN Ya Nuna Yadda Masu Bayyana Ra’ayoyi Suka Zargi Nuna Fin Karfi Da Amurka Ta Yi A Harkokin Intanet
- Chelsea Na Neman Sabon Gola Domin Tunkarar Sabuwar Kakar Wasa Ta Bana
Taron an gudanar da shi ne a Masallacin Sheikh Muhammadu Rabi’u da ke Goron Dutse, inda Khalifa Sheikh Muhd Nafi’u Isyaku Rabi’u ya jagoranta.
An kammala saukar karatun Alkur’ani sau 3,000 tare da yin addu’o’in samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da kuma neman tsira a wurin Ubangiji ya kawo saukin rayuwa da tabarbarewar tattalin arzikin kasa.
Sarki Bayero ya fito ne daga karamar fadar Nassarawa zuwa Masallacin Isyaku Rabiu da ke Goron Dutse, inda kuma ya sake amfani da hanyar da ya zo wurin komawa gida.