A cikin makon nan ne labarin fitar shararriyar ‘yar Tik-Tok dinnan wadda ake zargi da yawan kalaman batsa da rashin sanin ya kamata ta shiga hannun jami’an Hisbaar JIhar Kano bayan kwashe tsawon lokaci ana farautarta Bayan samun nasarar damke ta ne kuma hukumar HIsba ta gurfanar da ita gaban kotun shari’ar musulunchi dake Kwana Hudu a yankin Karamar Hukumar Nasarawa inda kotun ta aike da ita gidan gyaran halin na Kurmawa har zuwa ranar 20 ga wtan feburairin shekara ta 2024 domin ci gaba da sauraron karar.
A cikin dakon zuwan wannan rana da kotu ta ayyana domin ci gaba da sauraron karar ta Murja Ibrahim Kunya, sai kwatsam labarin fitar ta daga gidan gyaran halin ya fantsama akafafen sada zumunta, wanda haka ya haifan da zafafan martini tare da zargin hannu wasu masu mulki ko masu hannu da shuni da ake ganin sune suka yi duk mai yiwuwa wajen satar hanyar fitar da Murjar, sannan kuma aka ci gaba da cece ku ce a kafafen sada zumuntar wanda hakan ne ya ja hankalin bangarorin daban daban da ake kallo suna da ruwa da tsaki cikin lamarin.
- Firaministan Sin Ya Jagoranci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar
- Zaben Fitar Da Gwani Na APC A Edo Ya Bar Baya Da Kura
Tunda farko hukumar lura da gidajen gyaran hali na Jihar Kano ta bakin mai Magana da yawunta Musbahu Kofar Nasarawa Hukumar kula da gidajen ta musanta rahotanni cewa fitacciyar ‘yar Tik tok Murja Ibrahim Kunya ta gudu daga gidan yari.
Musbahu K/Nasarawa cewa ya yi Wasu rahotanni sun karade kafafen sada zumunta dake cewa Murja Kunya wadda kotu ta aike da ita gidan ajiya ranar Larabar da ta gabata bisa zargin ta da ayyukan badala da bata tarbiyya a kafafen sada zumunta ta tsere daga gidan gyaran halin.
Ta cikin wani sakon murya da ya aikawa kafafen yada labarai, mai magana da yawun hukumar Musbahu Lawal Kofar Nasarawa, ya ce an saki Murja bisa beli kamar yadda doka ta tanada bayan samun takarda daga alkali.
Ya kara da cewa yamadidin da ake cewar ta gudu daga Gidan gyaran Halin umarnin harbi ne akan duk wanda aka samu da laifin guduwa daga gidan gyaran hali, kuma takarda ce ta tsare Murja sannan takarda ce ta sake ta. Inji Musbahu Gwamnatin Kano
An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan zargin karya da ake ta yadawa a cikin al’umma musamman a kafafen sada zumunta na zamani kan zargin sakin wata fitacciyar ‘yar TikTok mai suna Murja Ibrahim Kunya daga gidan gyaran hali bisa yada abun da bai dace ba cikin bidiyo sabanin tanadin dokokin da suka dace a Jihar Kano.
A sanarwar da Kwamishinan yada labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ya sanyawa hannu, yace Wannan zarge-zargen kwata-kwata ba su da tushe balle makama, ba gaskiya ba ne, rashin sanin ya kamata ne kuma hasashe na wasu bata-gari da masu rashin kishin kasa da kishin Gwamnati da mutuncin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Idan dai ba a manta ba gwamnati ta san Murja Kunya ta gurfana a gaban wata Kotun Shari’a da ke Kwana Hudu a karamar Hukumar Nassarawa bisa zargin ta da yada wasu munanan faifan bidiyo a dandalin sada zumunta inda kotu ta bayar da umarnin tsare ta a gidan gyaran hali kuma zuwa ranar Talata, 20 ga Fabrairu, 2023 bayan ta saurari bukatar neman belin ta. Sai dai ya zo ma Gwamnati cewa an sake samun wani sabon zarge-zargen da aka yi mata wanda ya sa jami’an tsaro suka fitar da ita domin bincike. Har yanzu dai shari’arta na ci gaba da wanzuwa kuma za ta ci gaba har zuwa matakin karshe da kotu ta yanke.
Don haka ana kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi wa Gwamnatin jihar Kano a matsayin ba komai bane illa kokarin bata mata suna tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar abubuwan da aka tanadar a kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya. Inji Dantiye
A Halin yanzu haka Talatar Nan ne aka sake gabatar da Murja gaban kotu, Kuma tunda farar Safiya ita Murja ta halrci kotun, Kuma alkalin ya tambayi lauyanta inda ta amsa da cewar Yana hanya, Amma dai kotun tace ba zata jira zuwan lauyan nata ba, saboda haka sai kotun ta bada umarnin ga ma’aikatar Lafiya da akai Murja Asibitin domin bincika Kwakwalwar ta sannan ta bukaci Hukumar Hisba data ci gaba kulawa duk waniotsin Murja Ibrahim inda ta dage sauraron Shari’ar ta ta zuwa 20/5/2024.