Kotu ta yanke wa tsohon dan wasan Manchester City da Real Madrid Robinho hukuncin daurin shekaru tara a kasarsa ta Brazil bayan samunsa da laifin fyade a lokacin da yake taka leda a kasar Italiya.
Wata kotu a Italiya ce ta samu Robinho, mai shekaru 40 da haihuwa, a shekarar 2017 da laifin shiga cikin wani gungun maza da suka yiwa wata mata yar kasar Albania mai shekaru 22 fyade a 2013.
- Finidi George Ne Zai Jagoranci Wasan Sada Zumunta Na Nijeriya Da Kasar Mali
- Mbappe Ya Amince Ya Koma Real Madrid Akan Kwantiragin Shekaru 5 A Karshen Kakar Wasa Ta Bana
Alkalai a Brazil sun yanke hukuncin a ranar Larabar da ta gabata inda suka ce ya kamata a yanke hukuncin a Brazil bayan bukatar hakan da kasar Italiya tayi, amma Robinho zai kasance cikin ‘yanci har sai an gama shari’ar daukaka kara akan hukuncin, in ji lauyoyinsa.
Tsohon dan wasan na Brazil, wanda ya buga wa kasarsa wasa 100, yana buga wa AC Milan wasa ne a lokacin da ya aikata laifin, Robinho ya lashe kofunan La Liga guda biyu a cikin kaka hudu a Real Madrid, kafin ya koma City a kan kudi fam miliyan 32.5.