“A matsayina na babban jami’in zartaswa, ina ziyartar kasar Sin kusan a kowane rubu’in shekara saboda ina so in kasance kusa da kasuwar kasar Sin.” Roy Jakobs, babban jami’in zartaswa na kamfanin Royal Philips ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da wakilin CMG a lokacin bikin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na duniya wato CISCE karo na uku, da ke gudana a birnin Beijing na kasar Sin. Inda ya kara da cewa, halartar bikin baje kolin yana da matukar ma’ana ga kamfanin Royal Philips, kuma ba a iya rabuwa da tsarin samar da kayayyaki na Sin ba. Baya ga haka, ya ce kamfaninsa zai kara zuba jari ga kasar Sin a fannonin kirkire-kirkire da masana’antu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp