Takardar kudi dai abu ne da dokar kowacce kasa ta samar don a rika musayar kayayyaki da ayyuka da su bisa amincewar babban bankin kowacce kasa.
Sauya fasalin kudi ba sabon abu ne ba a kasashen duniya. Yana bayar da damar kara samar da tsaro ga kudin kasa ta yadda ba za a iya buga jabunsa ba. Sababbin takardun kudi suna zuwa da abubuwa hana daukan datti da za su kasance cikin yanayi mai kyau.
Kwanan nan Burtaniya ta kammala sauya fasalin kudinta na shekara biyar wanda aikin aka yi a watan Satumba 2022.
Sun nazarci cewa akwai alfanu sosai kawo takardun kudin daga Kasar Kanada wanda suke ci gaba da sanar da mutane shirin shekara biyu kafin a kaddamar da shi a shekarar 2016, wanda suka yi shi mataki-mataki.
A watan Disamba shekara ta 2021, Babban Bankin Turai ya bayar da sanarwar zai fara aikin sauya kudade. Zai tuntubi ‘yan kasa da suke kasashe 19 da suke amfani da kudin kafin su dauki mataki na karshe a shekarar 2024.
Wannan ba sabon abu ne ba ga Gwamnan Babban Banki wajen sanar da sake fasalin Naira. Kasa dai za ta amfana daga hana aikata abubuwan da ba su dace ba, kamar sace-sacen kudaden da rashin kin biyan haraji.
Sauya kudi zai sanya kudaden da aka sata su zama marasa amfani don mabarnatan ba za su iya zuwa bankuna su sanya bayanansu ba. Wanda suke kauce wa biyan haraji za su sauya kudin da suke da shi, kuma hakan ke nuna cewa hukuma za ta caje su yadda suke so.
Amma idan dai nufinsu gwamnatin tarayya rage mazambata da masu kauce wa biyan haraji, za a yi shi nesa da kofa a maimakon a bayar da sati 6 kacal. Tuni dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana cewa duk wanda ya kasa mayar da kudinsa cikin makonni 6 yana nuna cewa ya sami kudin ne ta haramtacciyar hanya.
Shin me hakan zai haifar na baci? shin suna sane da asarar da hakan zai haifar? Ko kuwa sun auna alfanun da za a samu ne kawai?
Tashin farko sakamakon da aka fara gani shi ne a kasuwar canji na kasashen waje, inda Naira ta fadi warwas kuma kullum faduwa take kara yi a kasuwar canji. Kudin da ba shi da daraja ba a iya amfani da shi don shigo da wasu abu na tattalin arziki da za a iya dogaro da shi, kasar za ta shiga wani yanayi mara dadi.
Yana yin kasuwanni da ake da su ya nuna cewa tattalin arziki da ake da shi bai farfado ba daga matsin da ya afka har sau biyu a cikin shekara 6.
A al’umma mai daraja, gwamnati takan damu matuka a duk lokacin da abubuwa suka kacame. Alal misali, Burtaniya ta amince dukkanin tsofaffin kudade a ko da yaushe za a sauya su zuwa sababbi a kowani lokaci da aka ware. Ana yin haka ne ta hanyar aikawa da su a gidajen aikawa da sakonni ko babban banki.
Haka kuma bankunan kasuwanci suna can suna sauyawa a duk lokacin da aka zuba kudi tsoho ba zai fita ba. Kasasshen Turai su ma suna irin haka wajen wannan tsarin, amma wasunsu suna da lokaci na tsawon shekara 5, yayin da wasu suke da dan kankanin lokaci.
Wannan sabon tsarin ya tuna da wani abu da ya faru a tarihi a shekarar 1984, wanda bai yi dadi ba. Littafan tarihinmu sun nuna cewa amincewar Buhari na sauya kudaden Nijeriya a shekarar 1984 ya taimaka wajen karyewar tattalin arziki, inda mutane da dama suka sami karayar arziki suka koma matalauta.
Abun damuwar shi ne, karayar arziki dole ta sami wadanda suka kasa sauya kudadensu kafin makonni shida su kare. Ba kamar yadda shugaban kasa yake tunani ba, mutane da yawa suna da halastaccen kudinsu da suka samu ta halas, amma wasu dalilai zai sanya ba za su iya sauya kudin ba a lokacin da aka ware. Yanzu dai muna dimokuradiyya, amma kasar kamar tsarinta ba na dimokuradiyya ba ce.
Idan za a iya tunawa wannan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya fitar da rahoton cewa yana kashe Naira biliyan 58 don buga takardun kudi na Naira biliyan 2.5 wanda a jumlance a watan Nuwamba 2021 an kashe Naira tiriliyan 1.1. Tun da kudaden da suke yawo a tsakanin mutane an bayar da rahoton akwai kusan Naira trilyan 3.2, hakan ya sa CBN ya kashe Naira biliyan 174 don buga kudi.
To shin Nijeriya tana samun kudaden shigan da suka kama daga harajin ko sabon kudi ne zai hana samun haramtattun kudade a kasa? Wannan kididiigan za a same shi daga yawan kudaden da suke yawo a hannun jama’a a wajen banki wanda ya kai na Naira tiriliyan 2.73.
Wani zai iya tunanin cewa wannan kudade ne masu yawan gaske, amma kudaden da suke yawo a hannun jama’a na kashi 6.5% na jimillar kudaden da suke kasar. Kudin da aka samar sun hada da dukkanin kudaden da suke yawo a tsakanin al’umma da wadanda aka ajiye su a bankuna da sauran cibiyoyin da ake aje kudade a asusun ajiyar CBN.
Wasu hanyoyin samar da kudade shi ne takardun shaida da bankuna suke samarwa.
A bayanan nan kudaden CBN da kididdigansu sun kai jimillar kudaden da Nijeriya ta samar a watan Agusta shekata ta 2022 na Naira tiriliyan 49.5.
Idan aka duba Buratniya tana da kashi 4% na jimillar kudaden da aka samar, a yayin da Amurka suke da kusan kashi 10% na kudaden da suke yawo a hannun mutane kamar yadda manyan bankunan kasashen suka bayyana. A duniya gaba daya muna da kashi 10% na kudaden da suke yawo a hannun mutane a kaso cikin 100 na kudaden duniya.
Duk da rashin karfin fasahar zamani a tsarin banki a Nijeriya, akwai kashi 6.55 na kudaden da suke hannun jama’a na jimillar kudaden da aka samar.
A farkon wannan shekara, wani kamfanin kididdigan sha’anin kudi mai suna, ‘PayPassage’ ya bayar da sanarwar cewa akwai mutum miliyan 59 wadanda suke balagagu da ba sa amfani da banki. A cikin masu amfani da bankin kuwa, kashi 73% ba su da cikakkun bayanai da za a bude masu babban asusun ajiya da za su karbi kudi masu yawan gaske, kamar BBN ko NIN ko bill ko lambar waya da sauran abubuwan da ake bukata.
Wannan kididdigan zai zama gaskiya idan muka tuna lokacin da aka dauka kafin a samar da NIN da BBN da ma katin jefa kuri’a a kwanan nan. A saboda haka mako 6 ya yi kadan wai a sauya kudi, in ba dai ana son a karya wadanda suka kasa sauyawa kafin lokacin da aka diba. Kuma mutane da yawa abun zai shafa.
Gwamnan CBN ya ce wannan tsarin zai taimaka wajen takaita kudaden a hannun jama’a wanda zai rage tsadar kayayyaki. Tsarin yana da kudurin rage buga kudade masu yawan gaske ba wai rage kason 6.5% na kudaden da suke hannaun jama’a ba.
A zahiri dai, tsadar rayuwa yana faruwa ne a tattalin arzikin samar da kudi yana tashi da sauri fiye da damar samar da ayyuka da kayayyaki. Tsadar rayuwa na iya karuwa in ba an samar da karin tsare-tsare da za su kara tattalin arziki wanda zai sanya a kara samun kudaden shiga.
Idan ana da karancin kudade a hannun jama’a kuma ana da mutane masu yawan gaske da ba su iya amfani da fasahar amfani da kudade a yanar gizo, ba za a taba samun abun da ake so cikin sauki ba. Tattalin arziki na buQatar kudade a hannun jama’a su rika kai kawo, musamman a kasa kamar Nijeriya.
Dole ne CBN ya buga kudi kamar Naira tiriliyan 3.2 don kauce wa tsaiko a ayyukan tattalin arziki wanda zai dauki lokaci mai tsawo kafin kasuwanci ya sauya ta amfani da kudi a hannu.
Kamar eNaira da CBN ya kasa gudanar da cikakken bincike a kansa kafin a soma aiki da shi. Abun da ake so a samu ba za a samu ba, wanda ya sanya tattalin arzikin fada wa cikin wani hali. Haka kuma wannan hange da aka yi ba a hango daidai ba kamar yadda aka yi wa tattalin arziki baki daya. Amma abun da ke faruwa a duniya shi ne zai taimaka wajen daukan matakai.
Matsalar tsarin Nijeriya shi ne, daukan mataki nan take a kan mutane wadanda ba su da gata. Wadanda suke yi wa Buhari fashin baki kan maganarsa na cewa masu samun haramtattun kudade, suna ganin kamar ana harin wasu ‘yan siyasa ne wadanda suke son siyan kuri’u a zaben 2023.
Idan wannan gaskiya ne, ire-iren wadannan mutane ba za su sauya tsarinsu ba? Za su sauya amfani da wasu kudaden ba na Nijeriya ba, amma wadanda ba su da gata za su iya karyewa. Wannan ya hada da kudaden da ake da su a waje wadanda za su kasance an yi asararsu don ba za su sami damar canzawa ba.
Idan gwamnati tana da karfi gyara kan halasta haramtattun kudade na dokar 2022, dole ta takaita yadda ake gudanar da amfani da kudade masu yawan gaske.
Dokar ta hana mutane masu zaman kansu da kungiyoyi daukan kudi tsaba da suka wuce Naira miliyan 5 da Naira miliyan 10, face sai ta amfani da cibiyoyin kudade. Haka kuma CBN na da mafi yawan kudin da za a cire na mutane masu zaman kansu da kungiyoyi. Wadannan tsare-tsaren sun isa ba sai an tilasta wa al’umma an kuntata masu da zai kai su ga yaki a siyasance ba.
Wannan tsarin ba dimokuradiyya ba ne, karfa-karfa ne kuma mutane za su ci gaba da sanya alamar tambaya game da lokacin da aka bayar da yadda za a kaddamar da tsarin.