Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Lahadin da ta gabata ya ce matakin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya dauka na kaddamar da sabbin kudade da kuma maye gurbinsu ya samu goyon bayansa kuma yana da yakinin cewa al’umar Nijeriya za su ci riba mai yawa ta yin hakan.
Da yake magana a hirar da gidan rediyon Hausa ya yi da fitaccen dan jarida Halilu Ahmed Getso, da Kamaluddeen Sani Shawai da aka gabatar da safiyar Laraba a Tambari TV, Shugaba Buhari ya ce dalilan da CBN suka ba shi sun tabbatar masa da cewa tattalin arzikin kasar zai ci gajiyar yin hakan da kuma samun saukin hauhawar farashin kaya da magance karakainar jabun kudi da kuma samun karin yawaitar kuɗaɗen da ke yawo cikin Al’uma.
- Da Dumi-Dumi: Bankin CBN Zai Sake Sauya Fasalin Naira N200, N500 Da N1,000
- CBN Da AMCON Sun Saka Bankin Polaris A Kasuwa
Ya ce bai dauki tsawon watanni uku na canjin sabbin takardun kudi a matsayin gajeren lokaci ba.
“Mutanen da ke da kudaden haram da aka binne a karkashin kasa za su fuskanci kalubale da wannan amma ma’aikata da kudaden kasuwanci ba za su fuskanci matsala ba.”
A cikin hirar, shugaban ya kuma yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi samar da abinci da tsaron kasa da dai sauransu.