Al’ummar garin Dankama da ke jihar Katsina sun shiga cikin makoki sakamakon mamakon ruwan sama da ya yi sanadin rugujewar katanga kuma ta afka kan yara biyar da mahaifiyarsu wadanda suka rasu nan take.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na safiyar ranar Litinin a gidan Muhammad Sani Garba Dankama, inda katanga ta murkushe su har lahira a cikin barcinsu.
- Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama Ɗalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah
- Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
An garzaya da wasu mutane uku da suka jikkata zuwa asibiti.
A cewar mahaifin marigayen, Dankama, ya bayyana cewa ba ya gida lokacin da katangar ta fado, inda ya ce ya kadu da jin labarin.
“Wannan lamarin ya faru da kusan mutane goma, amma mutane 6 sun riga mu gidan gaskiya. A yanzu haka, uku suna kwance a asibiti suna karbar magani,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp