ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Tuesday, July 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ƴansanda Sun Gano Motocin Sata 2 A Adamawa

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
Adamawa

Rundunar Ƴansandan jihar Adamawa ta bayyana cewa jami’anta sun gano motoci biyu da aka sace, tare da kama wani mutum mai suna Musa Suleh da ake zargi da satar.

Mai magana da yawun rundunar a jihar, SP Suleiman Yahaya, ya ce nasarar ta samu ne sakamakon bayanan sirri da DPO na Yola Division ya samu, wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin a Jambutu Motor Park da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa.

  • Jami’in Tsaro Ya Mayar da Dala 505 Da Riyal 30 Da Ya Tsinta A Yola
  • Sin Ta Sanar Da Cimma Nasarar Dashen Huhun Alade A Jikin Bil’Adama

A cewarsa, wanda ake zargin ya amsa cewa ya saci wata mota ƙirar Toyota Starlet mai lambar YLA-420 mallakar wani Babawo Abubakar na Ngurore, Yola ta Kudu. Haka kuma an gano wata mota ƙirar Toyota Starlet mai launin kore mai lambar JAL-861 CL a hannunsa, wadda bai gabatar da takardu ko hujjar mallaka ba.

ADVERTISEMENT

Kwamishinan Ƴansanda na jihar, CP Dankombo Morris, ya bayar da umarnin a miƙa shari’ar ga sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin zurfafa bincike da gano asalin motocin. Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa ba da bayanai cikin lokaci kan duk wani motsi da ya saɓa al’ada a unguwanninsu, tare da tabbatar da ƙudirin ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta ce bayan kammala bincike, ana sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu domin fuskantar shari’a.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina

Guguwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum Huɗu, Ta Yi Mummunar Ɓarna A Sokoto

Adamawa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir
  • Abubakar Sulaiman
    Shari’ar Malami Ba Za Ta Dakatar Da Burinsa Na Gwamna Ba, Inji Jam’iyyar ADC Ta Kebbi
  • Abubakar Sulaiman
    Kwamandojin Kungiyar Ansaru Biyu Sun Amsa Laifin Garkuwa Da Mutane A Kotu
  • Abubakar Sulaiman
    ICPC Ta Yi Karar Likitan El-Rufai Kan Ƙirƙirar Jabun Rahoton Lafiya

MASU ALAKA

Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina
Labarai

Sojoji Sun Daƙile Shirin Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wadanda Aka Sace A Zamfara Da Katsina

July 21, 2026
nema
Manyan Labarai

Guguwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutum Huɗu, Ta Yi Mummunar Ɓarna A Sokoto

July 21, 2026
Hadarin Kwale-Kwale
Labarai

Mutum Ɗaya Ya Mutu, Sama Da 30 Sun Ɓace A Hatsarin Kwale-kwale A Jigawa

July 21, 2026
Next Post
Gwamnan Neja Ya Kori Kwamishinoninsa Gaba Ɗaya

ICPC

Badaƙalar Binciken Hukumar Bogi: Gbajabiamila Ya Gurfana Gaban ICPC

July 21, 2026
Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

Sin Da Amurka Na Tuntubar Juna Game Da Inganta Mu’amalar Shugabanninsu A Bana

July 20, 2026
Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

Wang Yi: Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Manufofin MDD

July 20, 2026
Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

Mayar Da Muradun Jama’a A Gaban Komai: Daga Hikimar Da Aka Gada Tsawon Dubban Shekaru Zuwa Akidar Zamani

July 20, 2026
NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

NAFDAC Ta Kama Jabun Giya, Gurbataccen Abinci Da Motocin Man Kalanzir

July 20, 2026
Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

Karfin Sin A Bangaren AI Ya Samarwa Kasashe Masu Tasowa Damarmakin Cin Gajiyar Fasahar

July 20, 2026
Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

Sin Ta Zamo Kan Gaba A Duniya A Fannin Kirar Mutum-Mutumin Inji

July 20, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.