Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi.
A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma ba tare da wata matsala ba lokacin Chunyu da aka kammala jiya Asabar, alkaluman bana sun nuna an samu karuwar kashi 7.1 cikin dari a kan adadin da aka samu na daidai irin wannan lokacin a shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)