Kakakin rundunar ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA yankin gabashi Li Xi, ya ce a yau Litinin 14 ga wata, rundunar ta gudanar da atisayen hadin gwiwa na sojojin kasa, da na ruwa da na sama a kewayen zirin Taiwan, da arewaci da kudanci da gabashin yankin na Taiwan.
A cewar Li Xi, atisayen mai lakabin “Joint Sword-2024B”, wani mataki ne mai karfi na dakile ayyukan ‘yan aware dake neman ‘yancin kan Taiwan, kuma hakan mataki ne na wajibi, halastacce na kare ikon mulkin kasa da dunkulewar sassan ta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp