Rundunar sojojin ‘yantar da al’ummar kasar Sin reshen kudancin kasar, ta gudanar da ayyukan sintiri na dakarun sojin ruwa da na sama, a tekun kudancin kasar tsakanin ranaikun 3 da 4 ga watan nan.
Mahukuntan rundunar sun ce dakarunta na cikin shirin ko ta kwana a ko da yaushe, kuma a shirye suke su kare ikon mulkin kan kasa, da tsaro da hakkoki da moriyar kasa, kana suna da cikakken iko kan duk wasu ayyukan soji da ka iya haifar da hargitsi, ko jefa yankin na tekun kudancin Sin cikin yanayin zaman dar dar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp