Rundunar Sojin Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar wasu daga cikin jami’anta, sakamakon hare-haren da wasu ‘yan bindiga suka kai kan sansanonin sojin da ke Jihohin Neja da kuma Kaduna.
Hare-haren, sun faru ne a ranar Litinin, 24 ga Yunin 2025, a sansanonin sojin da ke Kwanar Dutse Mairiga da Boka a Jihar Neja da kuma Aungwan Turai da ke Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna kamar yadda rahotanni suka bayyana.
- Sanatan Neja Ta Arewa Ya Yi Allah Wadai Da Kashe Sojoji A Mariga
- Musayar Wuta Tsakanin Sojoji Da ‘Yan Bindiga Ta Ci Rayuka Da Dama A Jihar Neja
Har ila yau, rahotanni sun bayyana yadda ‘yan bindigar suka kai hari bangarori guda uku a lokaci daya, wanda hakan yasa dakarun sojojin mayar da martani ba tare da wani bata lokaci ba.
Rundunar ta bayyana wannan rahoto ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na sada zumunta da aka fi sani da D.
Kazalika, a yayin musayar wutar ne rundunar sojin ta tura dakarunta na kasa da kuma na sama, domin fatattakar maharan, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Rundunar ta bayyana cewa, an kashe ‘yan bindigar da dama yayin wannan gumurzu da ya dauki tsawon wasu awanni ana fafatawa da sojojin.
Koda-yake dai a cewar rundunar sojin, an kashe musu wasu daga cikin jami’ansu; yayin musayar wuta da ‘yan bindigar a daidai wancan lokacin.
Baya ga haka, rundunar sojin ta kuma kara da cewa; wasu sojoji hudu sun jikkata sakamakon harbin bindiga daga ‘yan ta’addar, amma kuma suna nan suna samun kulawa a asibiti.
Har wa yau, rundunar sojin ta kuma bayyana wadanda suka mutun a matsayin cikakkun Jarumai, wadanda suka tsaya tsayin daka, domin kare matsayinsu da kuma mutuncin kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp