Rundunar sojin saman Nijeriya ta yi asarar jiragen yakin 17 a cikin shekara 8, inda a 2023 ta yi asarar guda uku ciki har da wanda ya fadi ba tare ya raunata wani ba.
Haka kuma an samu haduran jiragen saman sojin Nijeriya 16 a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, wanda ya yi sanadin asarar jiragen sama 17 da sojoji 33.
LEADERSHIP ta rawaito cewa hatsarin na baya-bayan nan da ya rutsa da wani jirgin sama mai saukar ungulu kirar MI-171 na rundunar sojojin saman Nijeriya a ranar Litinin 14 ga watan Agusta, 2023 da misalin karfe 1:00 na rana a kusa da kauyen Chukuba a Jihar Neja.
An kiyasta kudin jiragen sun kai kimanin dalar Amurka 16.4 zuwa 18.4 kowannen su.
Mai magana da yawun rundunar sojin saman Nijeriya, Air Cdre Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jirgin ya taso ne daga makarantar firamare ta Zungeru zuwa Kaduna, amma daga baya aka gano cewa ya fadi a kusa da kauyen Chukuba da ke karamar hukumar Shiroro ta Jihar Neja.
Ya ce, “A halin yanzu ana ci gaba da kokarin ceto ma’aikata da fasinjojin da ke cikin jirgin, yayin da aka fara gudanar da bincike don gano musabbabin hadarin.”
Har zuwa sa’o’i 24 bayan faruwar lamarin, babu wani bayani kan kokarin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.
Yayin da Gabkwet bai amsa tambayoyin da aka yi masa ba kan karin haske dangane da hadarin, LEADERSHIP ta gano cewa jirgin na da ma’aikata hudu da suka hada da matukan jirgi biyu, injiniyan jirgi daya da kuma mai gadi daya.
Wani tsohon hafsan sojin sama ya shaida wa LEADERSHIP cewa hadarin jirgin babban illar ne a ayyukan sojin saman Nijeriya.
Wasu na iya zama sakamakon kuskuren matukin jirgin ne, ko injiniyoyi ko sauyin yanayin wanda ya rataya a kan shawarar matukin.
Ya ce tukin jirgin sama aiki ne da ke bukatar dukkan hankali don yin aiki daga maki A zuwa B.
A cewarsa, raba hankali yayin tuki yana kara janyo hadararruka. Ya kara da cewa tukin jirgin yana bukatar hatsuwa da hakuri.
A ranar 6 ga Fabrairu, 2023, wani jirgin saman sojin Nijeriya ya yi saukar gaggawa a Jihar Legas.
Jirgin mai lamba Cessna Citation CJ3, tayoyinsa sun makale yana cikin tafiya a Ilorin kuma dole ne ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Jihar Legas.
Sai dai a wannan hadari babu asarar rayuka ko jikkata ga ma’aikacin jirgin da kuma sauran mutanen da ke kasa.
A ranar 14 ga Yuli, 2023 wani jirgin horas da sojojin saman Nijeriya mai lamba FT-7NI ya yi hatsari a Makurdi ta Jihar Benuwai.
Jirgin ya yi hatsari ne a lokacin da yake atisayen horas da sojoji, amma dai matukan jirgin biyu sun tsira bayan da suka yi nasarar ficewa daga cikin jirgin.
Bugu da kari, babu asarar rayuka ko dukiyoyi a kusa da yankin da abin ya faru.
An samu hatsarin jiragen sama guda hudu a shekarar 2021, daya a shekarar 2022.
A ranar 21 ga Fabrairu, 2021, wani jirgin saman Nijeriya mai lamba NAF201 B350, ya yi hatsari a lokacin da yake komawa Abuja bayan da ya samu matsalar injin, inda ya kashe jami’an sojin sama bakwai nan take.
Haka kuma a ranar 31 ga Maris, 2021, jirgin saman rundunar sojin Nijeriya ya bace a Radar da ke Jihar Borno. Jirgin mai lamba NAF475 yana dauke da sojoji guda biyu.
Daga bisani sojojin Nijeriya sun gano tarkacen jirgin a dajin Sambisa bayan kusan shekara guda.
Hukumomin sojin saman Nijeriya sun bayyana sunayen matukan jirgin da suka hada da Laftanar Janar John Abolarinwa da kuma Laftanar Ebaykpo Chapele.
Har ila yau, a ranar 21 ga Mayu, 2021, wani jirgin saman sojojin saman Nijeriya ya yi hatsari a filin jirgin sama na Kaduna, inda ya halaka tsohon babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da wasu jami’ai 10 ciki har da ma’aikatan jirgin.
Haka kuma a ranar 18 ga Yuli, 2021, ‘yan bindiga sun bindige wani jirgin sama Nijeriya a Zamfara da misalin karfe 12:45 na rana, amma ba a samu asarar rai ba.
A ranar 29 ga Agusta, 2015, jirgin sama mai lamba 228 ya yi hadari, a ranar 10 ga Oktoba, 2015, wani jirgin yakin mai lamba FT-7NI ya fado.
A ranar 15 ga Nuwamba, 2016, jirgi mai saukan ungulu mai lamba 101 ya yi hatsari a Makurdi. A ranar 6 ga Yuli, 2017, wani jirgin sama mai saukar ungulu mai lamba 109 ya yi hadari, yayin da wasu jiragen FT-7NI guda biyu suka yi hadari a ranar 28 ga Satumba, 2018 a lokacin da ake atisayen.
Wani hatsarin jirgin saman ya afku a ranar 2 ga Janairu, 2019, inda ya rutsa wani jirgin sama mai saukar ungulu mai lamra mi-35.
Wani jirgin sama mai saukar ungulu na sojan Nijeriya ya yi hatsari a ranar 12 ga watan Yuni, 2019.
Jirgin saman soja mai lamba RB-GA ya yi hatsari a ranar 17 ga Agusta, 2019. A ranar 14 ga Nuwamba, 2019, jirgi mai lamba 109 ya yi hatsari.
Bugu da kari, wani jirgin mai lamba 350i ya yi hatsari a ranar 21 ga watan Fabrairun 2020. Jim kadan bayan faruwar lamarin, a ranar 31 ga Maris, 2020, wani jirgin Alfa ya bace a Jihar Borno.
Jirgin saman sojin Nijeriya kirar KingAir 350 ya yi hatsari a ranar 21 ga Mayu, 2021 yayin da wani jirgin Alfa ya yi hatsari a ranar 18 ga Yuli, 2021.
Har ila yau, wani jirgin Super Mushak mai horar da sojoji ya yi hatsari a Kaduna a ranar 19 ga Afrilu, 2022.