Kwamishinan ‘Yansandan jihar Nasarawa CP. Shattima Muhammad ya bayyanawa manema labarai rawar da Rundunar ‘yansandan jihar suka taka wajen kama masu aikata miyagun laifuka. Kwamishinan ya bayyana cewa rundunar ta kama mutum 9 tare da kwato harsasai 4,264 a wasu ayyukan sintiri da aka gudanar a ƙananan hukumomi 13 na jihar.
CP Shattima Mohammed, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a ofishin rundunar a Lafia, babban birnin jihar.
- Jarin Da Sin Ta Zuba Kai Tsaye A Kasashe Cikin Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Ya Karu Da Kashi 22.9% A 2024
- Nan Gaba TIinubu A Wajen Opay Da Moniepoint Zai Nemi Rancen Kuɗi – Dino Melaye
Yayin da yake bayyana alkaluman a babban birnin jihar, Lafia, CP Mohammed ya ce, “A ranar 7 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 6:30 na yamma, bisa sahihan bayanan sirri cewa, wasu da ake zargin masu safarar makamai daga jihar Benuwe sun isa wani daji da ke iyakar Kadarko, a karamar hukumar Keana , suna sauke makamai da harsasai domin rarraba wa abokan harkarsu.
“Da samun rahoton, babban jami’in ‘yansanda na yankin, ya jagoranci tawagar jami’an ‘yansanda kai tsaye zuwa wurin.
“Da suka hango jami’anmu, sai suka ajiye kayan suka tsere cikin daji. Binciken wurin ya haifar da gano makaman nan: bindigogi AK-49 guda huɗu, bindigogi AK-47 guda uku, bindiga G3 guda ɗaya, bindiga ƙarama (Sub-Machine Gun) guda ɗaya, mujallu harsasai guda goma sha ɗaya, harsasai 7.62mm guda 4,046, harsasai 5.5mm guda goma sha ɗaya, harsasai 38mm guda 132, da harsashi guda 75.”
CP Mohammed ya ƙara da cewa, a wani samame da aka yi ranar 6 ga Satumba, 2025, bisa bayanan sirri, an kama wani mutum mai suna John Paul daga Abuja a tashar motar Akwanga-Wamba yayin da yake kan hanyarsa zuwa Abuja. Da aka binciki jikinsa, an gano bindigogi biyar kirar gida, kuma wanda ake zargin ya bayyana cewa da akwai abokan harkansa. Tuni ‘yansanda suka bazama nimansu.
Haka kuma da misalin ƙarfe 3:00 na dare jami’an da ke ofishin ‘E’ Division a Shabu, cikin Lafia, sun kama manyan masu ƙera bindigogi biyu, James Philip da Alpha Philip, dukkansu maza ne daga unguwar Faferuwa, Lafia.
“Bincike ya kai ga kama manyan masu saye da sai da bindigogin da aka kirar gida , waɗanda suka haɗa da Usman Abubakar daga Shendam Road, Lafia Yakubu Danladi daga Mararaba Akunza, Lafia; Usman Kasimu wanda aka fi sani da Bobo daga Bukan Sidi, Lafia; da Abdullahi Adamu daga Bukan Sidi, Lafia.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun haɗa da: bindigogi dogaye guda 13, bindigogi ƙanana guda 10, bindiga Revolver guda ɗaya, takuba guda uku, Rigunan sanye na ƴan sanda guda uku da hulun su, injinan ƙera bindiga guda uku da kayan aiki,
Yayin da yake yabawa jajircewar jami’an sa, CP Shattima Mohammed ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawar da miyagun mutane a Nasarawa.
Ya ce, “Ina kira ga kowa ya kasance mai lura, mai bin doka, kuma ya rika bayar da bayanai ga Rundunar yan sanda.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp