Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta sanar da kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne kuma dan fashi da makami da yin garkuwa da Mai Anguwar Garun Babba, Alhaji Abdulmumini Mudi Zakari.
A cewar wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ranar Asabar, jami’an rundunar yaki da masu garkuwa da mutane ne suka cafke wani matashi mai suna Usman Lawan Baba, mai shekaru 27, wanda aka fi sani da “Yellow,” a ranar 2 ga Oktoba, 2025, a Dakatsalle, Zango Ranka, a karamar hukumar Bebeji ta jihar Kano.
- Al’ummar Sokoto Sun Koka Kan Yadda Hare-haren Lakurawa Ke Kara Ta’azzara
- Me Yarjejeniyar Kawo Karshen Yakin Gaza Da Amurka Ta Tsara Ta Kunsa?
Sanarwar ta ce, an bayyana wanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Agustan 2023 da ake nema ruwa a jallo, yayin da aka yi garkuwa da wani mai anguwan kauye tare da kwace naira miliyan 2.75, wayar Tecno Kevo 4, da agogon hannu.
Daga baya jami’an ‘yansanda suka ceto basaraken bayan sun tare hanyar da ‘yan bindigar ke bi wajen tserewa.
Yayin da ake yi masa tambayoyi, Yellow ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, kuma ya amince ya karɓi ₦6,000 a matsayin kason sa na kudaden da aka sace. Ya kuma bayyana sunayen sauran abokan aikinsa, wadanda tuni wasu daga cikinsu suka gamu da ajalinsu a batakashin da suka yi da hukumomin tsaro.














