Rundunar ‘yansandan jihar Yobe ta kama wani malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta Al-Ma’arif da ke karamar hukumar Potiskum a jihar Yobe bisa zargin yi wa wata daliba fyade.
An ce malamin, ma’aikaci ne a babban asibitin jihar Potiskum da kuma Al-Ma’arif – kwalejin kimiyyar lafiya mai zaman kanta da ke Potiskum.
- Kakakin Taron Majalisar NPC: Sin Za Ta Ci Gaba Da Kokarin Kare Ikonta Na Mallakar Yankunan Kasa
- Ƙanin Ɗan Majalisar Zamfara Ya Shaƙi Iskar Ƴanci A Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, DSP Abdulkarim Dungus ya sanya wa hannu, ta tabbatar da cewa, jami’an ‘yansanda sun kama Hudu a ranar Larabar da ta gabata, inda ya ce, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano hakikanin zargin da ake yi masa.
Dungus ya kara da cewa, Hudu wanda yanzu haka ke hannun ‘yansanda, an kama shi ne bisa zargin aikata laifin fyade, cin zarafi da kuma cin amana.
Magatakardan kwalejin, Usman Alhaji Saleh, ya tabbatar wa manema labarai lamarin,.