• English
  • Business News
Sunday, July 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rusau: Kungiyoyi Sun Bukaci A Hana Gwamnan Kano Shiga Amurka

by Sadiq
2 years ago
in Labarai
0
Rusau: Kungiyoyi Sun Bukaci A Hana Gwamnan Kano Shiga Amurka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wasu kungiyoyin fararen hula sun rubuta takardar koke ga Amurka da Tarayyar Turai inda suke neman su hana Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf izinin shiga kasashensu.

Sun kuma rubuta makamancin wannan korafin ga China da sauran kasashe.

  • Ta Ya Za A Magance Rashin Tsaftar Yara Mata Masu Tasowa?
  • Muhimmancin Kafa Cibiyar Kulawa Da Lafiyar Hakori

Kungiyoyin, wadanda ke karkashin inuwar Gamayyar Samar da Shugabanci Nagari (CGGCI) sun ce sun yi kiran ne saboda abin da suka kira yawan rushe-rushen da gwamnan ke yi tun da ya hau mulkin Jihar.

A wata takardar korafi da Shugaban Kungiyar na kasa, Kwamared Okpokwu Ogenyi, ya sanya wa hannu, kungiyar ta bukaci a hana Gwamnan da iyalansa da kuma shugabanni da mambobin jam’iyyarsa ta NNPP izinin saboda abin da suka kir take hakkin dan Adam da sunan rusau.

Kwafin takardar korafin dai da aka raba wa manema labarai ranar Asabar, ya yi zargin cewa yayin rusau din, an yi asarar rayuka da na dukiyar sama da Naira biliyan 200.

Labarai Masu Nasaba

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

Kungiyoyin sun kuma yi zargin cewa da gangan Gwamnan yake rusau din saboda ya goge duk ayyukan alherin da tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi lokacin da yake mulkin Jihar.

“A kan haka ne muke so a hana shi, tare da dukkan Shugabannin jam’iyyarsa ta NNPP a matakin Jihar da ma kasa baki daya, izinin shiga kasashen. A halin yanzu, wannan ne kawai abin da za a yi masa don ya shiga taitayinsa,” in ji kungiyoyin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Abba Kabir YusufAmurkakanoKungiyoyiRusau
ShareTweetSendShare
Previous Post

Ta Ya Za A Magance Rashin Tsaftar Yara Mata Masu Tasowa?

Next Post

Bikin Baje Kolin Cinikayya Ya Zama Dandalin Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Related

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 
Wasanni

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

1 hour ago
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta
Labarai

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

3 hours ago
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson
Siyasa

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

6 hours ago
An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
Manyan Labarai

An Kama Mutane 4 Da Ake Zargi Da Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja

7 hours ago
‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Labarai

‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki

8 hours ago
Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
Rahotonni

Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu

9 hours ago
Next Post
Bikin Baje Kolin Cinikayya Ya Zama Dandalin Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Bikin Baje Kolin Cinikayya Ya Zama Dandalin Karfafa Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

LABARAI MASU NASABA

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata 

July 26, 2025
Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa

July 26, 2025
Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya

July 26, 2025
Kasar Sin Na Tir Da Harin Isra’ila Kan Makarantu A Gaza Tare Da Kira Da A Dakatar Da Bude Wuta

Isra’ila Na Sanya Alamar Rusau A Dubban Gidajen Fararen Hula A Gaza

July 26, 2025
Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

Firaministan Sin Ya Halarci Taron Kasa Da Kasa Game Da Jagorancin AI

July 26, 2025
Amurka

Natijojin Auren Dattijo Ga Budurwa

July 26, 2025
An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

An Yi Bikin Karbar Fitilar Gasar Wasannin Kasa Da Kasa Ta Shekarar 2025 A Chengdu

July 26, 2025
Tarihin Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (6)

Dalilan Da Suka Sa Cinikin Bayi Bai Yi Nasara A Arewacin Nijeriya Ba

July 26, 2025
Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

Sin Ta Gudanar Da Gasar Kirkire-kirkire Ta Daliban Kasa Da Kasa A Yankin Afirka Karo Na Farko

July 26, 2025
Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

Duk Da Ni Ɗan Adawa Ne Buhari Ya Hana A Murɗe Min Zaɓe — Dickson

July 26, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.