Ma’aikatar bayar da qgajin gaggawa ta babban birnin tarayya (FEMD) ta bayyana cewa an ceto mutane 105, yayin da rayuka huɗu suka salwanta sakamakon jerin hadɗarurrukan rushewar gine-gine a fadin birnin tarayya a shekarar 2024.
Muƙaddashin daraktan FEMD, Injiniya Abdulrahman Mohammed, ya bayyana wannan a taron manema labarai da aka gudanar ranar Litinin a Abuja. Ya bayyana cewa rushewar gine-ginen ya faru a unguwannin Prince and Princess Estate, da Guzape District, da Garki 2, da Kubwa, da Sabon Lugbe kusa da hanyar tashar jirgin sama.
- Mutum 10 Sun Mutu A Turmutsutsin Rabon Shinkafa A Abuja
- Wike Ya Bai Wa Asibitocin Gwamnati Umarnin Tallafa Wa Wadanda Turmutsitsin Abuja Ya Rutsa
Mohammed ya ƙara da cewa FEMD ta fuskanci manyan matsalolin da suke buƙatar taimakon gaggawa a wannan shekarar, ciki har da rushewar gine-gine, da gobara, da ambaliyar ruwa, da girgizar kasa, da rabon kayan tallafi ga waɗanda abin ya shafa. Ya ce a cikin shekarar, an ceto mutane kimanin 3,500 daga yanayi daban-daban na gaggawa, tare da amsa kiran gaggawa 165 ta layin wayar su mai sauƙin kira, 112.
Ya kuma bayyana cewa FEMD ta fara amfani da fasahar zamani wajen inganta tsarin gudanar da agaji. Wannan yana ƙunshe da amfani da tauraron ɗan Adam mai zagaya ƙasa don samun hotuna da bayanai na zahiri da za su taimaka wajen tantance haɗurruka da rage matsaloli a birnin tarayya. Mohammed ya yi kira da a ƙara amfani da sabbin dabaru don magance matsalolin da ake fuskanta a cikin birnin nan gaba.