Da safiyar ranar Lahadi ne dakarun Rasha suka harba makami mak linzami zuwa birnin Kyiv na Ukraine, a wani mataki na ci gaba da mamayar kasar.
An jiyo karar ababen fashewa a sassa daban-daban na birnin Kyiv din.
- Da Alamun Daliban Kano Ba Zasu Rubuta NECO A Bana Ba Kan Bashin 1.5 Da Ake Bin Gwamnatin Kano
- 2023: An Bukaci INEC Ta Dakatar Da Tinubu Kan Zargin Rashin Takardun Karatu
Magajin birnin, Vitali Klitshko, ya ce tuni motocin daukar marasa lafiya hade da ma’aikatan ceto suka isa wurin.
Harin na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya sake kira ga aminan Ukraine su kai musu daukin makaman kare sararin samaniyar kasarsa.
A bidiyon da ya ke wallafa a kowanne dare tun bayan fara yakim, Mista Zelensky, ya ce yakin da suke yi da Rasha ya shiga wani mataki mai sosa rai da tsananin wuya, bayan Rasha ta karbe birnin Severodonetsk.
Yakin dai ya faro ne tun a watan Fabrairun 2022, wanda yanzu ya kawo sama da watanni 4 ke nan ana gwabzawa.
Yakin ya yi sanadin rasa rayukan dubban mutane daga tsagin Ukraine da Rasha, ciki har da manyan dakarun sojin kasashen biyu.