Babban hafsan sojin kasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba, makiyan kasar nan za su fara Ɗanɗana kuɗarsu duba da da irin tasirin sabbin dabarun yaki da ta’addanci da aka bullo da su a rundunar sojin Nijeriya.
Oluyede ya bayyana haka ne a Bauchi a ranar Talata jim kadan bayan wani atisayen gwajegwajen makamai da aka gudanar a cibiyar ajiye makamai ta Victor Kure, a yayin rufe bikin horas da jami’ai yadda ake amfani da makamai na 2025.
- Xi Jinping Ya Karfafawa Matasa Gwiwar Daukar Nauyin Daukaka Zamanantar Da Kasar Sin
- ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
COAS, wanda ya samu wakilcin kwamandan Ordnance Corps, Manjo Janar Henry Wesley, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta riga ta sayi kayan aiki da makamai masu yawa domin kara tunkarar duk wani nau’in tada kayar baya da ta’addanci da ya addabi kasar nan.
Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp