Ko ina ka duba kwana nan, ana ta magana a kan yadda sabbin matakan gwamnatin Donald Trump ke tayar da zaune tsaye a harkokin kasuwancin duniya. To, sai dai kuma ga dukkan alamu, kaikayi zai koma kan mashekiya sakamakon wata sanarwar da kungiyar manoman Amurka ta fitar a kan yadda lamarin zai dagula lissafin ’ya’yanta.
An yi hasashen cewa, amfanin gonar da Amurka ta fitar waje a shekarar 2024 ya kai na dala biliyan 170.5, kuma kasashen da Trumph ya ayyana kara wa haraji: Sin, da Mexico da Canada su ne kan gaba wajen sayen amfanin gonar na Amurka da kashi 49.9 cikin 100. Don haka, manoman suka ce, sanya karin haraji kan kasar Sin da sauran manyan masu shigo da amfanin gona na Amurka zai kawo masu cikas.
- ‘Yansanda Sun Cafke Baƙin Haure 165, An Miƙa Wa Hukumar NIS A Kebbi
- Matsalar “Fentanyl” Ba Laifi Ne Da Amurka Za Ta Iya Dora Wa Wasu Ba
Duk da Trump yake, a ranar Talatar nan, ya ce zai dakatar da harajin kashi 25 a kan Mexico da Canada na tsawon wata guda, amma kuma kasashen ba za su amince ba domin sun san Trump “mage ne mai kwanciyar daukar rai”.
Manoman Amurka da suka koka da lamarin a karkashin kungiyarsu ta cinikayyar amfanin gona, sun ce, dama suna ta faman kaka-ni-ka-yi a cikin tsadar fitar da kayayyaki, da raguwar farashin amfanin gona, kana ga kalubalen samar da wadataccen abinci a duniya. A yanzu kuma, karin harajin na Amurka zai kara dagula lamarin a yawancin yankunan karkarar Amurka saboda su ma kasashen da abin ya shafa ba za su rungume hannu su zura ido suna kallon ruwa kwado ya yi masu kafa ba.
A cewarsu, “karin harajin zai kuma jefa manoman Amurka cikin hasara sannan ya bai wa abokan gasarmu na Kudancin Amurka da sauran sassan duniya damar yi mana fintinkau ta hanyar karbe cinikinmu daga abokan kasuwanci saboda tsadar da kayanmu za su yi.”
“Canada, Mexico da Sin su ne suke sayen rabin duk kayayyakin amfanin gona da Amurka ke fitarwa. Kasuwanni ne da muke bukata babu makawa don raya tattalin arzikin Amurka. Sanya haraji kan manyan kasuwannin fitar da kayayyakin guda uku na noma da kiwo na Amurka, musamman na dogon lokaci zai haifar da mummunan sakamako,” in ji sanarwar.
Tabbas! abin da manoman suka fada gaskiya ne, domin ko a shekarar 2018, karin harajin da Amurka ta kakkaba a kan kayayyakin kasar Sin, ya janyo kasar ta Sin wadda a baya ita ce ta fi shigo da wake na Amurka, ta sanya karin harajin kashi 25 cikin 100 na ramuwar gayya kan kayayyakin da Amurka ke fitarwa. Kuma a yanzu ma, Sin ta lashi takobin mayar da martani inda tuni, a farkon makon nan ta fitar da sanarwa daga ma’aikatar cinikayya da ma’aikatar kudi a kan fara aiwatar da martaninta ga Amurka.
Daga ciki, kasar Sin ta sanya harajin kashi 10% zuwa 15% kan wasu kayayyakin da ake shigowa da su daga Amurka, wanda zai fara aiki daga ranar 10 ga Fabrairun nan. Sannan, Sin ta yanke shawarar shigar da rukunin kamfanonin US PVH da Illumina a cikin jerin kamfanonin da ba su da tabbas. Kana ta shigar da kara a gaban Kungiyar Kasuwanci ta Duniya, watau WTO. Bugu da kari, Sin ta hana fitar da wasu sinadarai masu muhimmanci da ake amfani da su wajen hada kayayyakin lantarki da na karafa.
Fitina dai a kwance take, kuma la’ana tana kan duk wanda ya tayar da ita! (Daga Abdulrazaq Yahuza Jere)