Yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale wajen gano cutar tarin fuka, watau TB, da warkar da ita da kuma rigakafinta a duniya, asibitin kula da lafiyar kirji na Beijing ya kaddamar da wasu sabbin fasahohi na zamani, inda hakan ya kara kuzari tare da kawo sabon ci gaba a kokarin da duniya ke yi na dakile cutar.
Nasarorin da aka samu sun kunshi daukar samfuri ba tare da an shigar da wani abu a jikin mara lafiya ba, da binciken gano cutar ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira ta AI, da gajarta tsarin jinyarta, da kuma gwajin maganin rigakafinta na mRNA, wadanda suka zama wani gagarumin ci gaba a yakin da kasar Sin ke yi da cutar TB.
- Kwalara Ta Kashe Mutum 14, Ana Zargin 886 Sun Kamu A Nijeriya – NCDC
- Boko Haram Ta Kashe Sojoji A Wani Sabon Hari A Borno
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), cutar TB ta kashe mutum miliyan 1.25 a duniya a shekarar 2023, sa’ilin da aka samu wasu sabbin mutane da suka kamu miliyan 10.8 duk dai a shekarar. A kasar Sin kuwa, an kiyasta cewa, sabbin mutanen da suka kamu da cutar sun kai 741,000, yayin da kuma mutum 25,000 suka mutu a shekarar ta 2023.
Shugaban asibitin kula da lafiyar kirji na Beijing, Li Xiaobei ya bayyana cewa, sabbin fasahohin da aka samu tun daga kan binciken gano cutar ba tare da shigar da wani abu jikin mara lafiya ba har zuwa maganin rigakafi na mRNA, za su sake fasalin dabarun magance cutar ta tarin fuka.
Li ya kara da cewa, bisa yadda mutum miliyan 350 suka kamu da cutar a duniya, ci gaban kimiyyar da kasar Sin ta samu ya bullo da wata muhimmiyar hanyar samar da makoma ta kawar da cutar ta TB daga doron kasa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp