Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin ko NBS ta nuna a yau Asabar cewa, sabbin sassan dake ingiza bunkasuwar kasar Sin sun kara samun kuzari a shekarar da ta gabata, yayin da kasar ke ci gaba da kokarin raya tattalin arziki da karfafa fasahohin kirkire-kirkire.
Hukumar ta NBS ta ce, kididdigar sabbin sassan dake ingiza bunkasuwa da hukumar ta tattara, ta karu da kashi 19.5 cikin dari daga shekarar da ta gabata zuwa kashi 119.5 a shekarar 2023.
Lyu Haiqi jami’i a hukumar ta NBS ya ce, wannan karuwar na nuni da sabbin sassan dake ingiza bunkasuwar kasar, wadanda suka hada da sabbin masana’antu, da sabbin salon kasuwanci da sabbin samfuran kayayyaki, sun ci gaba da samun bunkasuwa a shekarar da ta gabata, kuma kasar ta samu daidaiton ci gaba wajen bunkasa tattalin arzikinta da samun bunkasuwa bisa sabbin fasahohin kirkire-kirkire. (Mai fassara: Yahaya)