Auwalu Lawan Aranposu, Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa a Jihar Kano, ya yi zargin cewa, dakatarwar da aka yi masa, siyasa ce kawai da nufin farantawa wasu ‘yan siyasa rai.
A wata hira ta musamman da ya yi da jaridar Nigerian Tracker, Aranposu ya bayyana cewa, har yanzu bai samu wata sanarwa a hukumance dangane da dakatar da shi ba.
Ya tabbatar da cewa, akwai takun-saka tsakaninsa da wasu ‘yan majalisar zartaswar ta Kansilolo wacce ta a kai ga yanke hukuncin dakatar da shi daga mukaminsa.
A cewar Aranposu, majalisar ta dakatar da shi ne sabida zargin alakarsa da Kwankwasiyya, kungiyar siyasa a jihar.
Ya bayyana cewa, an zarge shi da biyayya ga Kwankwasiyya lokacin da ya nuna adawa da matakin tsige mataimakin shugaban karamar hukumar..
An zabi Auwal Aranposu ne a karkashin jam’iyyar APC a shekarar 2021 a lokacin gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje na APC.
Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44, duk suna karkashin Jam’iyyar APC ne inda ake sa ran za su kammala wa’adinsu a watan Janairun 2024.