Idan muka dubi girman ranar haihuwar Annabi (SAW), Idi ne na Musulmi na murnar haihuwar shiriya, Manzon Allah ya zo ya shiryar da halitta bakidaya, ya tserar da ‘Ya’yan Adam daga wuta zuwa rahama, kamar yadda Allah ya ce “kuna gabar wuta dab ku rubza (Annabi) ya tserar da ku daga gareta”.
Manzon Allah (SAW) ya ce, “misalina da ku, kamar mutumin da ya kunna wuta ne yana jin dimi a daji (sai kwari su zo suna son fadawa ciki shi kuma yana karesu) sai ku zo za ku fada ciki, ni na kama kubakar zaninku na jawo ku.” To, ka ga ranar haihuwar wannan alherin babu wanda zai manta da ita musamman duk wanda alherin ya sama. Allah ya ce wa Manzon Allah (SAW), “Ba mu aikoka ba face kai rahama ne ga halitta bakidaya,” duk abin da ba Allah ba, yana cikin wannan halittar. Ka ga ranar haihuwar wannan, dole duk wanda ya san wannan rahama ta shafeshi ya yi murna.
Maganar da ta fi shahara ita ce an haifi Manzon Allah (SAW) ranar 12 ga Rabi’ul Auwal, a shekarar Giwa.
Larabawa ba a taba aiko wani Annabi daga cikinsu ba, don haka ba su yin lissafi sai da wannan shekara da aka haifi Annabi (SAW). Kamar misali yanzu, nasara suna ba da tarihin abubuwa da shekarar haihuwar Annabi Isah (AS), yanzu sun ce muna shekara ta 2019 da haihuwarsa. To kuma duk abin da aka yi kafin nan, sukan ce an yi abu kaza kafin haihuwar Annabi Isah (AS) da shekara kaza, ma’ana dai da haihuwar Annabi Isah suka riki tarihi. To, su ma Larabawa an yi musu wani abu da dole su riki tarihi da shi.
An yi wani kasaitaccen Sarkin Habasha (Ethiopia), Abarahata. Ya tambaya wai me ya sa Larabawa suke girmama wannan daki na bulolluka (Ka’aba)? Aka ce Kakansu ne ya gina musu (a matsayin) Dakin Allah.
Ai fa sai ya yi kasaitaccen gini mai kyau da kayan alatu iri-iri, ya ce a fada wa Larabawa su zo su rika kewaya wannan da ya gina yanzu. Wani Balarabe ya ce ka ji shashasha, ai dakin na addini ne kuma ana la’akari da waye ya gina, Annabi Ibrahim ne ya gina wannan, mu ba kyale-kyalen kudi ne muke dubawa ba.
Shikenan wani Balarabe ya tafi wancan dakin da Sarkin ya gina ya bata shi da gudawa. Sai Sarkin ya ji haushi ya ce yanzu ba da wannan Balaraben zai yi ba, Ka’abar da a kanta ne aka bata masa gini, da ita zai yi, zai je ya rusheta.
Sarkin ya shirya ya tsallaka ta wutsiyar Baharmaliya da rundunarsa ciki har da giwaye. A cikin giwayen akwai wani da ake kira da Mahmuda a ciki. A lokacin Larabawa babu yadda za a yi su iya yaki da shi.
Sai manyansu suka tafi wurin Kakan Manzon Allah, Abdulmuddalibi su ji ya za a yi da wannan Sarki, suka ce yanzu haka za mu barshi ya rusa Ka’aba?, Abdulmuddalibi ya ce musu to ya za mu yi? Amma ni dai na yi imani dakin nan akwai mai shi (Allah) kuma ba zai bari a rusheshi ba. Wannan yana daga cikin imanin Kakannin Manzon Allah (SAW).
Yana da kyau idan mutum yana da ikon kare wani abu ya yi, amma idan bai da iko sai ya yi imani irin na Abdulmuddalibi. Sarkin nan ya yi ta bude hanya da yaki har ya iso Makka ya yi sansani a kusa da Arfa. Ya sa wata bataliya ta je ta kai wa cikin Makka hari, akwai rakumar Abdulmuddabili kusan 200 da ake kiwo aka kora su zuwa wurin Sarkin.
Da masu kiwo suka shaida wa Abdulmuddalibi abin da ya faru sai ya yi shiri ya tafi wurin Sarkin. Da Abdulmuddalibi ya isa can, mutanen Sarkin suka ce wa Sarkin yauwa, wannan dama shi ne shugaban mutanen Makka kuma dakin ma (Ka’aba) a hannunsa yake. Abdulmuddalibi yana shiga wurin Sarkin; da Sarkin ya ga kwarjinin hasken Annabi (SAW) a fuskar Abdulmuddalibi nan da nan ya mike ya zaunar da shi a gadonsa. Ya tambaye shi, Dattijo me ya fau, me kake so? Abdulmuddalibi ya ce rakumana guda 200 da rundunarka ta kore mun su ne na zo ka bani.
Sarkin ya ce ka bani kunya, yadda na ji tsoronka na ga girmanka a zuciyata, da ka ce in koma kar in taba dakin nan (Ka’aba) sai in koma. Abdulmuddalibi ya ce, abin ya fi karfin duk wannan. Rakuma nawa ne, Daki kuma akwai mai shi.
Abarahata ya ce a ba Abdulmuddalibi rakumansa kuma ya shaida masa cewa gobe zai zo ya rusa Dakin Ka’aba. Abdulmuddalibi ya yi kasida ya ce Allah ga garinka, ga dakinka nan ka karesu. Ya ce mutanen Makka duk su hau dutse.
Da rundunar Sarkin ta taso, aka bugi Giwar nan ta yi hanyar Makka sai kawai ta durkushe, aka yi duka, aka yi duka ta ki. Amma idan aka karkatar da ita hanyar dawowa teku sai ta yi tafiya, da an juya hanyar Makka kuma sai ta ki. Sai Allah ya taso da tsuntsaye suka yi musu ruwan duwarwatsu na wuta, Allah ya sanyasu kamar karmami abin cinyewa. Allah ya yi kaca-kaca da su kamar irin yadda shanu suke cinye karmami su tattaka su yi kashi a kai.
Akwai wani mai jan wannan giwar da shi bai mutu ba saboda ya yi imani, kuma ya rayu ya yi tsawon rai.
An yi wani abu da aka tuna tarihin kin shigar giwan nan Makka, lokacin da Manzon Allah (SAW) ya aika Sayyidina Usman zuwa cikin Makka aka ga bai dawo ba, ya nemi Sahabbai su yi mubaya’a, matukar an kashe Sayyidina Usman za a shiga Makka da yaki. An shirya an yi komai aka tayar da rakuminsa (SAW) sai ya ki tafiya, Manzon Allah ya ce wa Sahabbai su kyale rakumin, wanda ya tsare Giwar nan daga shiga Makka shi ya tsare Rakumin.
To sai ya zama da wannan alheri na halakar da rundunar Abarahata da Allah ya yi, Larabawa suke kirga shekarun tarihi suka sa wa shekarar sunan Shekarar Giwa. Sai ya zamo a wannan shekarar ce kuma aka haifi Manzon Allah (SAW). A lokacin kuma an yi shekara 570 da haihuwar Annabi Isah (AS). Idan lissafin Muharram za a yi kuma sai ya zama da wata uku kenan a shekarar giwa, tun da daga farkon Muharram din zuwa Rabi’ul Auwal wata uku ne.
Allah ya nuna girman haihuwar Manzon Allah (SAW). Shehu Ibrahim Inyass (RA) yana cewa, bayan karatuttuka, bayan hujjojin Mauludi, ita kanta duniya ta yi Mauludi, sandararrun abubuwa ma sun yi, don haka wane mai hankali ne zai tsaya cewa duk da wadannan sai an kuma ba shi wata hujja a kan Mauludi? Hatta gumaka sai da suka kife, sai dai daga baya aka sake kafa su.
Katangar Kisra (wadda take kasar da babu wadda ya kaita karfi a wancan lokacin, wato super power) da aka ce babu abin da zai rusheta ta tsattsage har bangwayenta 14 suka daddare. Kambun Sarkin Kisra aka tunkude shi.
Wutar Farisa da suke bauta mata shekara dubu ba ta taba mutuwa ba, ita ma ranar da aka haifi Manzon Allah (SAW) ta mutu. Koramar Sawata da ba a taba ganin ta kafe ba ita ma rannan ta kafe. Aljannu ma sun yi ta rera wakoki na murna, Larabawa masu gane wakokinsu a wancan lokacin ma sun haddace wakokin.
Duniya ta yi haske, Allah ya yi wani irin na’urar satellite har aka rika ganin gine-ginen birane masu nisa daga Makka duk kuwa da cewa garin Makka a kwari yake ba a kan tudu ba. Aka kori Aljannu daga wuraren da suke zuwa satar jin magana a sama, da sauran alherorin da aka gani ranar haihuwar Manzon Allah (SAW).
Duniya ta zamo namiji saboda haihuwar Gwarzon Namiji a cikinta (SAW).
To, duk wadannan alheran idan aka gwamasu da batun murnar shekarar Hijira ai ko burbushin murnar Hijirar ba za a gani ba, don haka Sahabbai suka ware ta Hijirar daban, ta haihuwar Manzon Allah (SAW) aka barta daban.