Kwamishinan almuran addini na Jihar Kano, Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya bay-yana cewa kishin ilimi ne ya sa gwamnatin jihar karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf ta kaddamar da raba wa makarantu firamare da sakadare littattafan karatu sama da miliyan 2.
Sheik ya ce gwamnatin Kano babban burinta shi ne bunkasa ilimin tun daga firamare har zuwa jami’a, hakan ce ta sa aka kaddamar da raba litattafai, sannan kuma an tantance daliban da za a tura karatu wajen.
- Kasar Sin Za Ta Kammala Aikin Layin Dogo Daga Abuja Zuwa Kano Da Fatakwal Zuwa Maiduguri
- ‘Yansanda A Kano Sun Musanta Zargin Daukar Masu Laifi Aiki
A cewarsa, an biya wa yara maarasa karfi kudin karatu sama da dubu 7 a jami’ar Bayero ga kuma ragin kashi 50 cikin 100 na kudin makarantar da daliaban Kano za su biya a kowacce babbar makaranta mallakar gwamnatin Kano, wannan ma ki-shin ilimi ne na gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf.
A karshe, Sheik Auwalu ya ce wannan gwamnati ba ta bar kowanna bangare ba wajen tallafa wa al’ummar Kano. Ya ce a wannan lokaci rabon tallafi na abinci wanda ya hada da shinkafa da masara buhuna a kowacce mazaba 484 a kananan hukumomin 44 a na Jihar Kano.