Kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC), ta shiga yajin aikin gargadi a jihohi 14 da kuma babban birnin tarayya, Abuja, biyo bayan gazawar da gwamnatocin jihohin suka yi wajen fara biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000.
Wasu daga cikin jihohin da yajin aikin ya shafa sun hada da Kuros Ribas, Enugu, Nasarawa, Katsina, Sakkwato, Zamfara da kuma Kaduna.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 9, Sun Sace Wasu A Sakkwato
- CMG Ya Gabatar Da Alamar Bayyana Kyakyyawar Fata Ta Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Kasar Sin
Shugaban kungiyar NLC reshen jihar Kaduna, Kwamred Ayuba Magaji Suleiman, ya bayyana cewa ma’aikatan sun yi biyayya ga uwar kungiyar wajen tsunduma yajin aikin.
Kwamred Ayuba, ya ce sun yi hakan ne domin bai wa ma’aikatansu kariya kamar yadda doka ta tanada.
Sai dai ya ce har yanzu babu wani martani daga bangaren gwamnati game da yajin aikin da suka tsunduma, amma kofarsu a bude ta ke domin tattaunawar samun masalaha.
Tun a ranar 10 ga watan Nuwamba, NLC ta bayar da wa’adin ranar 1 ga watan Disamba kafin shiga yajin aikin gargadin.
Tuni dai wasu ma’aikata a jihohin da yajin aikin ya fara, suka fara karbar mafi karancin albashi.
An kai ruwa rana dai kafin a sasanta tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin NLC da TUC game da tsayar da mafi karancin albashin ma’aikata a Nijeriya.