A cikin shekaru 60 da suka gabata, kasashen Sin da Faransa sun raya ingataccen hadin gwiwa a fannoni da dama, da suka shafi makamashin nukiliya, da jirgin kasa mai saurin tafiya, da sararin samaniya, da aikin gona, da kiwon lafiya da dai sauransu, wadanda suka samar da fa’ida ta zahiri ga jama’ar kasashen biyu.
A halin yanzu, Sin da Faransa dukkansu suna kan kololuwar matsayi a tarihin ci gaban kasa. Kasar Sin ta hanzarta samar da sabon tsarin ci gaba, da neman bunkasuwa mai inganci yayin da ta mai da hankali matuka kan muhimman batutuwa da suka hada da bunkasa sabon tsarin samar da hajoji da hidimomi masu karko, da sabunta tsarin masana’antu, da farfado da yankunan karkararta, da samar da ci gaban hadin gwiwa a shiyya. yayin da ita kuma kasar Faransa take fama da batutuwa masu mahimmanci, gami da sauyin makamashi, da sauyi zuwa hada-hadar dijital da karuwan tsofaffi.
- Manzon Musaman Na Shugaba Xi Jinping Ya Halarci Taron Koli Na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi Karo Na 15
- An Gabatar Da Shirin Bidiyo Mai Suna Labarun Da Xi Jinping Ya Fi So A Wasu Muhimman Kafafen Yada Labaran Faransa
A wannan halin sauye-sauye da duniya ke fuskanta kamata ya yi bangarorin biyu su hanzarta yin hadin gwiwa a fannonin bunkasa fasahar kere-kere, da tattalin arzikin dijital, da masana’antun masu kiyaye muhalli, da ci gaba mai dorewa, da kara inganta hadin gwiwar aikin gona. Wannan yunkurin zai karfafa hadin kai tsakanin tsarin gudanar da masana’antu, saukake samar da jari da habaka mu’amalar ma’aikata, da zaman lafiya.
Bisa gayyatar da shugaba Emmanuel Macron na Jamhuriyar Faransa, da shugaban kasar Serbia Aleksandar Vucic, da takwaransa Tamas Sulyok da firaministan kasar Hungary Viktor Orban suka yi masa, shugaba Xi Jinping zai kai ziyarar aiki a kasashen Faransa, Serbia da Hungary daga ranar 5 ga watan Mayu zuwa 10. Ana sa ran ziyarar ta shugaba Xi a Faransa za ta haifar da wani sabon kuzari ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Faransa a fannonin da na ambato, tare da ba da jagoranci ga kasashen biyu wajen gano sabbin fannoni da hanyoyin hadin gwiwa cikin kankanin lokaci.
Shekaru 60 da suka gabata, janar de Gaulle ya bijirewa matsin lamba na kasashen yammacin Turai, ta hanyar kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Faransa. Inda daga bisani ya yi hasashen cewa “Hakika a bayyane yake cewa, dole ne Faransa ta yi mu’amala ta fahimtar juna da Sin kai tsaye, kuma ta tabbata kasar Sin ta yi mu’amala da ita”, wanda hakan ya jadadda jaruntaka, jajircewa, da hikimar da ke da ma’ana a duniyarmu ta yau. (Mohammed Yahaya)