Yayin zaman tattaunawa na zagayen Turai da Asiya mai taken “Sabon ci gaban kasar Sin, da sabbin damammaki na duniya” wanda kafar CGTN karkashin babbar kafar gidajen rediyo da talabijin na Sin, wato CMG ya gudanar a jiya Alhamis a birnin Beijing, wasu masana annoba, da masana kan batun kasa da kasa, da masana tattalin arziki daga Sin, da Rasha, da Kazakhstan, sun yabi Sin bisa manufarta ta kyautata manufofin rigakafi da shawo kan annobar COVID-19 sosai.
Sassan sun kuma fitar da hakikanan abubuwan da suka faru ad bayanai filla filla sun kalubalanci zargi, da shakku da wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka bayyana a kwanakin baya domin yunkurin bata sunan kasar Sin. Sannan masana da suka halarci taron tattaunawa sun mayar da martani ga matsalolin da suke jawo hankulan wasu kasashen duniya.
Bugu da kari, a yayin tattaunawar, masana sun sa ran kan yadda kasar Sin za ta taka karin rawa wajen daidaita harkokin kasa da kasa, da batutuwan diflomasiyya dake kasancewa tsakanin manyan kasashen duniya, da kuma farfadowar tattalin arziki da dai sauransu.
Taron dandalin tattaunawa na Turai da Asiya da ta gudana a nan birnin Beijing, dandali ne na daya daga cikin jerin tarukan tattaunawa da gidan talabijin da CGTN ke gabatarwa, inda a kan gayyaci ’yan siyasa, da masana na Sin, da na yankunan Turai da Asiya da su tattauna, da yin mu’ammalar ra’ayoyi kan abubuwa masu daukar hankali dake shafar yankuna daban daban na duniya ta kafar yanar gizo ko a zahiri. Wannan ne kuma karon farko da aka gudanar da dandalin na tattaunawar talabijin a shekarar 2023. (Safiyah Ma)