Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa ya ce inganta dakin gwaje-gwaje da hukumar ta yi zai kara inganta aikin NDLEA wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi a Nijeriya.
Marwa wanda ya bayyana haka a wajen kaddamar da sabon dakin gwaje-gwaje na hukumar da aka gyara a Legas.
- Shekarau Ga Tinubu: Ka Rage Yawan Ministocinka Domin Rage Kashe Kudade
- NDLEA Ta Cafke Wani Tsoho Mai Shekaru 67 Dauke Da Hodar Ibilis A Filin Jirgin Saman Abuja
Ya ce, “Da wannan wurin, yanzu muna sa ran samar da na’urorin gwaje-gwaje da binciken kwa-kwaf na zamani, wadanda za su inganta gwaje-gwaje na aiki da mafi kyawun tsari, wanda hakan zai habaka hanyoyin nazarin tushen shaida a cikin bincikenmu.”
Shugaban hukumar NDLEA wanda daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi ya wakilta a wajen taron ya jaddada muhimmancin dakunan gwaje-gwaje na zamani don samun nasarar yaki da miyagun kwayoyi a kasar nan.
A cewarsa, duk wanda ya san muhimmancin dakin gwaje-gwajen magunguna zai aminta da cewa bincike yana taka muhimmiyar rawa wajen gano munanan sinadaran da ke boye a cikin miyagun kwayoyi da kuma illolinsu.
Shugaban na hukumar ya ce a shekaru uku da ya yi, hukumar ta yi nasarar kwato tan 7,590 na miyagun kwayoyi. Ya ce wadannan miyagun kwayoyi sun hada da wadanda doka ta ayyana da kuma sabbi wadanda dokokin kasashe ba su ayyana ba, har ma da wadanda aka kwaba sinadarai a dakin gwaje-gwaje na sirri.
Marwa wanda ya yaba wa gwamnatin kasar Amurka bisa daukar nauyin aikin, wanda ya hada da inganta dakin gwaje-gwaje, dakin tambayoyi da kuma samar da dakin karatu na yanar gizo, ya kuma yaba wa hukumar UNODC bisa nata kokarin a fanninta.