Daga Abba Gwale
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce, gwamnan jihar Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, zai sake yin nazari akan hanyoyin da akabi wajen tsige sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi na biyu.
A cikin wani fefen video da yake yawo a kafafen sada zumunta, Kwankwaso ya ce, cire sarki da raba masarautun Kano abu ne wanda yakamata a sake yin nazari a kansu idan sabuwar gwamnati ta fara aiki.
“Munyi yakin neman zabe kuma kowa yasan muna da jama’a a Nigeria musamman jihar Kano, kuma yanzu mun sake dawowa zamu ci gaba da ayyukan alheri da gwamnatin mu ta bari a baya domin wannan sabon gwamnan da masu taimaka masa zasu ci gaba” in ji Kwankwaso, wanda shine madugun darikar Kwankwasiyya.
Ya ci gaba da cewa ” a matsayin mu na manya zamu ci gaba da basu shawara suyi abinda ya kamata, munyi kokari mu shiga maganar cirewa da nada sarki, amma yanzu lokacin mu yazo”
Ya kara da cewa ” Wadanda suka samu dama yanzu zasu zauna su kalli lamarin, zasu kalli abinda yakamata suyi, ba wai kawai sarki ba ita kanta masarautar an rarraba ta gida biyar saboda haka duka sai anyi nazari akai, yawanci shugaba yana gadar abubuwa masu kyau da marasa kyau masu wahalar gyarawa”
A ranar 9 ga watan Maris ne na shekarar 2020 gwamnan Kano mai barin gado Abdullahi Umar Ganduje ya cire Muhammad Sanusi na biyu bayan da tun farko aka raba masarautun Kano gida biyar.
Sai dai gwamna Ganduje ya taba bayyana cewa bai taba yin da-na-sanin cire sarkin ba.