Sin da ASEAN sun rattaba hannu kan sabunta yarjejeniyar ciniki ta “3.0” ta yankin wato “Sin-ASEAN Free Trade Area 3.0”, yayin taron shugabannin Sin da ASEAN karo na 28.
Ra’ayoyin kasa da kasa sun nuna cewa wannan nasarar ta nuna alkawarin da Sin da ASEAN suka yi na ci gaba da goyon bayan kasancewar bangarori daban-daban a duniya da tsarin kasuwanci mai ‘yanci, kuma ta kafa wata sabon muhimmin mataki na kara hadewar tattalin arzikin yankin, wanda zai kara karfafa huldar kasuwanci ta duniya, kuma ya zama abin koyi.
A matsayin farkon yarjejeniyar ciniki ta ‘yanci da Sin ta kulla da wata kungiya, sabunta sigar yarjejeniyar ciniki ta Sin-ASEAN zuwa 3.0 wato “Sin-ASEAN Free Trade Area 3.0” ta jawo hankalin duniya. Idan aka kwatanta da sigar 1.0 a shekarar 2010 wacce ta mayar da hankali kan ‘yantar da cinikin kayayyaki, da sigar 2.0 da ta fara aiki a shekarar 2019 wacce ta fi mayar da hankali kan saukake cinikin ba da hidima da zuba jari, sigar 3.0 ta dace da sabbin yanayin kasuwanci na duniya, ta fadada fannoni masu tasowa, da kara bude kasuwa gaba daya, da kuma inganta ci gaban da ya hada da kowa. Wadannan sun hada da bangarori na yanzu na yarjejeniyar ciniki ta Sin-ASEAN, da kuma sabbin fannoni kamar tattalin arzikin fasahar zamani, da tattalin arziki mara gurbata muhalli, da hadin gwiwar samar da kayayyaki.
Zhai Kun, mataimakin shugaban kungiyar nazarin yankin kudu maso gabashin Asiya na Sin, kuma farfesa a jami’ar Peking, ya bayyana cewa, tun daga sigar 1.0 zuwa 2.0 har zuwa 3.0, an samu ci gaba mai zurfi ta hanyar sabbin ka’idoji na fasahar zamani da kare muhalli, da sabunta tsarin amince da ka’idojin juna, da kara karfin hadin gwiwar samar da kayayyaki, inda ya inganta yankin ciniki daga matsayin “kara adadi” zuwa “ingantacciyar bunkasa”. A yayin da ra’ayin bangaranci da babakere ke takura tsarin hadin gwiwa na duniya, wannan sabon tsarin ya samar da wata hanya iri ta Asiya don kiyaye tattalin arzikin duniya mai bude kofa. (Amina Xu)














