Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansanda ta ƙasa (NPF), CSP Benjamin Hundeyin, ya nemi ƙarin haɗin kai tsakanin ƴan jarida da rundunar ƴansanda domin ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma gina amincewar jama’a.
Hundeyin ya yi wannan kira ne yayin ziyarar da ya kai sakatariyar ƙungiyar ƴan jarida ta Nijeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya, Abuja, ranar Juma’a. Ya bayyana cewa aikin sa a matsayin mai magana da yawun rundunar ba zai yiwu ba tare da cikakken goyon bayan kafafen yaɗa labarai na.
- ‘Yansanda Sun Ceto Wani Dan Shekara 25 Da Aka Sace A Jihar Kebbi
- An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
Ya jaddada muhimmancin tatattun rahotanni, yana mai gargaɗin cewa labarai na ƙarya ko wanda ba’a tace ba kan iya lalata amincewar jama’a ga rundunar ƴansanda. “Ƴansanda ba za su iya kasancewa a ko’ina lokaci guda ba, shi ya sa bayanai daga jama’a ke da matuƙar muhimmanci. Amma idan jama’a suka rasa amincewa da mu, waɗannan muhimman bayanai kan ɓace,” in ji shi.
A nata jawabin, shugaban NUJ a FCT, Comrade Grace Ike, ta yaba da wannan ziyara, tana mai cewa yana nuna sha’awar rundunar wajen buɗe tattaunawa kai tsaye da ƴan jarida. Ta jaddada cewa NUJ ba ta lamunci cin zarafi ko tsoratar da ƴan jarida ba, tare da bayyana cewa ƙungiyar za ta haɗa hannu da rundunar wajen yaƙi da labaran ƙarya da inganta rahotanni masu amfani ga jama’a.
Hundeyin ya kuma yi alƙawarin cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da ba da amsa cikin adalci idan ƴan jarida suka gamu da matsaloli a yayin aiki.