Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa, sabuwar hukumar da aka kafa ta kamfanin mai na kasa, za ta ceto makamashin kasar nan, tare da tabbatar da cewa ana amfana da makamashin kamar yadda ya kamata.
An kafa sabuwar hukumar ce domin a tabbatar da hanyoyin samar da makamashi a wannan kasa.
Da yake jawabinsa, a wannan taro mai dimbin tarihi, a dakin taro na Fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce, babban kamfanin main a Afirka zai tallafa wajen fanin na makamashi da kuma man fetur a wannan kasa.
Haka kuma shugaban kasa Buhari, ya ce, wannan wani babban abin tarihi ne da ba a taba yi ba a kamfanin samar da mai na kasa ba, saboda haka muke fatan wannan abu ya taimaka wajen kara bunkasa tattalin arzikinmu da habaka rayuwar al’ummar wannan kasa.
Haka kuma shugaban kasar ya ce, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kula da samar da hanyoyin da kamfanin man zai ci gaba da bunwasa, yadda zai samar wa da al’ummar kasar nan hanyoyin bunkasa rayuwa.
Sannan kuma, shugaban kasar, ya gode wa ‘yanmajalisa, bisa cikakken goyon bayan da suke ba shi, wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi ci gaban kasar nan.