Sabon Kwanturolan hukumar kula da shige da fice (NIS) da aka tura jihar Ribas, CIS Sunday James, ya kama aiki gadan-gadan a shalkwatar hukumar da ke jihar tare da shan alwaashin inganta nagartar aiki a kowani lokaci.
Da ya ke ganawa da manyan jami’an hukumar a jihar ta Ribas, ya ja hankalinsu a kan bin matakan aiki tare da ka’idoji, kana ya bukaci kowani jami’in hukumar da ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata yayin zaben 2023 da ke tafe ta hanyar gudanar da aiki bisa kwarewa da bin ka’idoji da dokokin aiki.
Sunday James ya gargadin dakarun nasa su nesanci shiga harkokin siyasa, yana mai cewa aikin da ke gabansu shi ne sanya ido da tabbatar da an gudanar da zaben nan cikin kwanciyar hankali kuma sahihi, amma kada wani a cikinsu ya nuna bangaranci ta siyasa a yayin da ke bakin aikinsa.
James ya tabbatar da cewa, NIS reshen jihar Ribas a shirye take wajen gudanar da aikin zaben 2023 kuma za ta tabbatar dukkanin wadanda ba ‘yan Nijeriya ba, ba su samu shiga cikin harkokin zaben Nijeriya na 2023 ba, “Aikinmu shi ne mu tabbatar ‘yan kasashen waje (Wadanda ba ‘yan Nijeriya ba) ba su yi mana kazalandan a zaben 2023 ta hanyar ganin ba su samu damar jefa kuri’a ba.”
A wata sanarwar da sashin yada labarai na hukumar a jihar Ribas ya fitar a ranar Talata, ya bayyana cewar, manyan jami’an hukumar da suke shiyya-shiyya na hukumar a kananan hukumomi 23 da ke jihar sun hallara a shalkwatar inda sabon kwanturolan ya musu cikakken bayanin yadda za su kauce wa nuna bangaranci a siyasa kuma ya umarni su je su fada wa sauran jami’an da ke karkashinsu a kowani mataki domin tafiyar da aiki bisa ka’ida.
“Kwanturolan ya kuma shaida wa jami’an da su kasance cikin shiri tare da daukan matakan da suka dace na tsaro hadi da gaggawar kai rahoton abubuwan da ka iya tasowa domin daukan matakan da suka dace a kan lokacin domin inganta aikin da aka tura su a yayin zaben.”
Sanarwar ta kara da cewa, “Mista James ya amshi ragamar hukumar ne a hannun tsohon kwanturola, AJ Kwassau wanda yanzu aka masa karin girma zuwa mataimakin kwanturola janar ACG kuma yanzu haka shi ne mai kula da sashin bai wa ‘yan kasashen waje izinin aiki a kamfanoni da zuba hannun jari a Nijeriya (CERPAC) a shalkwatar hukumar NIS da ke Abuja.”