Sabon Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) reshen Jihar Legas, CIS Bala Dangana ya karɓi ragama tare da fara aiki nan take a ranar Alhamis 6 ga Yulin 2023.
Manya da ƙananan jami’ai na reshen jihar ne suka yi kwamba domin yi wa sabon Kwanturolan lale marhabin a Babban Ofishin NIS na Jihar Legas.
CIS Bala Dangana wanda ya kaɓi ragama daga CIS Mani Bagiwa, ana sa rai zai yi cikakken amfani da basira da ƙwazonsa wajen magance matsaloli da tsaikon da masu neman fasfo ke fuskanta a wannan shiyyar.
Kafin karɓar gamar Legas dai, CIS Bala Dangana, ya yi aiki a matsayin Babban Jami’in Fasfo na Fatakwal da ke Jihar Ribas. Haka nan ya taɓa zama Shugaban Sashen Tabbatar da Ingancin Aiki a Shalkwatar NIS da ke Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp