A yau ne aka kawo karshen bikin baje kolin ciniki ta yanar gizo ko Internet, karo na 2 a birnin Hangzhou dake gabashin kasar Sin. A wajen bikin da ya gudana a kwanakin baya, wani saurayi dan kasar Najeriya ya janyo hankalin kafofin watsa labaru daban daban. Sunansa Usman Ahmad Ustaz, wani mai tallata kayayyaki ta yanar gizo ko Internet ne.
A lokacin bikin da ya gudana a Hangzhou, kamfaninsa ya kafa wata rumfa a wajen bikin, inda Usman da abokan aikinsa suka tallata wasu tufafin wasan motsa jiki ga mutanen dake kasashen waje, ta hanyar watsa bidiyonsu a kai tsaye. A cewar Usman Ustaz, ko da yake ya yi karatu a kasar Sin tare da samun digiri mai alaka da aikin likitanci, amma yanzu ya ga dimbin damammaki da ke akwai a fannin kasuwanci ta yanar gizo ko Internet.
- Sin Na Karfafa Matakan Samar Da Hidimomin Kudi Ga Kamfanoni Masu Zaman Kansu
- Jami’ar MDD: Sin Mai Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Tattalin Arzikin Zamani Na Duniya
Ya ce, yana son koyon fasahohin kasar Sin ta fuskar ciniki ta yanar gizo, sa’an nan a nan gaba zai bude wani kamfani a Najeriya, ta yadda zai iya amfani da fasahohin da ya samu don raya tattalin arziki a can.
Dalilin da ya sa Usman Ustaz ya zabi kasar Sin don ya zama wurin fara sana’arsa, shi ne ya gane ma idanunsa yadda harkokin ciniki ta yanar gizo ko Internet ke samun bunkasuwa cikin matukar sauri. Yanzu haka, kasar Sin ta rike matsayi na farko a duniya a fannonin yawan cinikin da ake yi ta yanar gizo, da yawan kudin da ake biya ta wayar salula. Kana a fannin ciniki ta hanyar watsa bidiyo kai tsaye ta yanar gizo, ko a birnin Hangzhou da Usman yake da zama kadai ma akwai kamfanoni masu alaka da hakan fiye da 5000, da yawan mutanen da suke aiki a wannan fanni fiye da miliyan 1.
Ban da haka, kasar Sin, bisa matsayinta na kawar kasashen Afirka, wadda ke kokarin aiwatar da manufar “rikon gaskiya, da samar da hakikanin alfanu, da kauna, da sahihanci”, yayin da take hulda da kasashen Afrika, tana son raba fasahohinta ga abokananta dake nahiyar Afrika. Yanzu idan ka samu damar ziyara a jami’o’i da makarantun koyon ilimin sana’a dake wurare daban daban na kasar, za ka ga dimbin daliban kasashen Afirka da suka zo kasar Sin don samun horo kan ilimin ciniki ta yanar gizo, wadanda za su zama kwararrun da nahiyar Afrika ke bukata don raya tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani.
Ban da taimakon kasashen Afirka a fannin samar da kwararru, kasar Sin tana kuma kokarin ba da taimako a fannin kafa dandalin da ake bukata, a lokacin da ake neman raya ciniki ta yanar gizo a kasashen Afrika. A shekarar 2014, wani kamfanin kasar Sin ya kafa wani dandalin kasuwanci na yanar gizo ko Internet, da ake kira Kilimall a Afrika, wanda ke samar da hidimomi a kasashen Kenya, da Uganda, da Najeriya. Kuma a yanzu haka, yana samun karbuwa sosai tsakanin al’ummun kasashen.
A halin yanku, akwai kamfanoni ko daidaikun mutane fiye da 8000, na kasashen Afrika da Sin, da suka bude kantuna fiye da dubu 12 kan shafin yanar gizo na Kilimall, inda suke sayar da kayayyaki nau’o’i kimanin miliyan 1. Haka zalika, ko a kasar Kenya kadai, Kilimall ya bude kantuna fiye da 1000, wadanda ake iya dudduba kayayyaki, da karbar kayan da aka saya, inda aka samar da guraben aikin yi fiye da dubu 10.
Sa’an nan, ban da dandali na kasuwanci, kasar Sin ta zuba jari a nahiyar Afrika, don bude dandali na biyan kudi ta yanar gizo ko Internet. Misali, a Najeriya, wasu kamfanonin Sin sun ba da taimako, a kokarin kafa wasu dandalin biyan kudi mafiya samun karbuwa da ake kira da PalmPay, da Opay.
Za mu iya tunanin makomar bangaren ciniki ta yanar gizo a nahiyar Afrika: A nan gaba, duk lokacin da wani ya samu bukatar sayen kaya, ko kayan gida, ko tufafi, ko wani nau’in abinci da yake bukata, to, zai dauki wayar salula ya duba, don kwatanta kayayyaki iri-iri da mabambantan kantuna ke samarwa, sa’an nan ya zabi kayan da ya fi inganci da araha, wanda ya samu mafi yawan yabo daga mutanen da suka taba amfani da shi, don ya biya kudi da yin oda kai tsaye ta wayar salula.
Kana a nasu bangare, masu shaguna suna iya nuna kayayyakinsu kan dandalin ciniki ta yanar gizo cikin sauki. Wani lokaci ma, suna iya watsa wani bidiyo kai tsaye kan shafin Internet don tallata kayayyakinsu. Ta la’akari da yadda ake kokarin raya yankin ciniki mai ’yanci na nahiyar Afrika ko AfCFTA, nan gaba ’yan kasuwar Afrika za su iya samun karin oda daga kasuwannin kasashe makwabta. Kana matasa za su samu sauki a fannin neman aikin yi, saboda karuwar kananan kamfanoni masu kula da kasuwanci ta yanar gizo, da dimbin guraben aikin yi da kamfanonin jigilar kayayyaki za su samar.
Wadannan abubuwa za su zama hakikanin yanayin da ake ciki, saboda su ne abubuwan dake faruwa a kasar Sin, bayan ta samu ci gaban bangaren ciniki ta yanar gizo ko Internet. Kana yayin da kasar Sin ke ba da taimako don raya ciniki ta yanar gizo a nahiyar Afrika, kamfanonin kasar su ma za su samu dimbin damammaki na zuba jari, da raya harkokinsu, ta hanyoyin ciniki, da kula da dandalin ciniki, da daukar nauyin wasu manyan ayyuka, da dai sauransu.
Yadda ake zuba jari a nahiyar Afrika, da ba da taimako a fannin raya sabbin sana’o’i a can, tare da tabbatar da moriyar kai, wannan ya dace da muradun kasar Sin na hadin kai don cin moriya tare, gami da neman samun ci gaba na bai daya. (Bello Wang)