Babban sakataren kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), Kwamared Joseph Ajaero, ya zama sabon shugaban kungiyar kwadago ta kasa NLC.
Kwamared Ajaero an tabbatar dashi ne a matsayin shugaban kungiyar a karshen taron majalisar wakilai ta kungiyar karo na 13 da aka yi a Abuja a ranar Laraba.
A jawabinsa na karbar shugabancin NLC, ya sha alwashin fitowa zanga-zanga tare da ‘ya’yan kungiyar a kan matsalar karancin kudin Naira idan gwamnati ta gaza yi wa ‘yan kasa cikakken bayani kan magance matsalar nan da karshen mako mai zuwa.