• English
  • Business News
Saturday, May 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sabon Shugaban PDP Na Katsina Ya Nemi Haɗin Kai A Tsakanin ‘Ya’yan Jam’iyyar

by El-Zaharadeen Umar
2 years ago
in Siyasa
0
PDP
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sabon shugaban jam’iyyar PDP mai adawa a jihar Katsina Alhaji Lawal Ɗanɓaci ya yi kira ga sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar da su zo a yi aiki tare domin samun nasarar zaɓe a shekarar 2023.

  • Hedikwatar Tsaro Ta Ayyana Neman ‘Yan Ta’adda 19 Ruwa A Jallo, Ta Sa Ladar Miliyan 5 Kan Kowanne

Alhaji Lawal Ɗanɓaci ya yi wannan kira ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kaɗan da shigarsa ofis a matsayin sabon shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina wanda uwar jami’yya ta ƙasa ta naɗa

A cewar sa, ya hango nasara da duk wasu sharuɗa na cin zaɓe a shekarar 2023 shi yasa yake neman hadin kan ya yan jam’iyyar ta PDP domin yin aiki tare.

A cewar Alhaji Lawal Ɗanɓaci ya zo wannan shugabanci ne da kyakkyawan niya shi yasa ya ce duk inda ɗan PDP yake ya zo a dunkule waje guda.

Ya kara da cewa alamun nasarar da ya hango sun haɗa da yadda jami’yyar APC mai mulki ta jefa jama’a na yunwa da rashin tsaro da bala’o’i iri daban daban ya isa misalin abinda zai faru idan an zaɓe.

Labarai Masu Nasaba

Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye

Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi

Alhaji Lawal Ɗanɓaci ya kafe akan cewa kowa yasan jami’yyar PDP jam’iyya ce ta adalci da girmamawa tare da ba kowa hakkin sa.

Sai dai ya cigaba da cewa zamba cikin aminci da yaudarar da jami’yyar APC ta yi al’umma a ƙasa da kuma jihar Katsina, jama’a na jiran ranar zaɓe domin zartar da hukunci daidai da laifi.

“insha’Allahu a shugabancina babu wani ɗan mowa ko ɗan bora zan kwatanta adalci wanda shi ne ginshikin cigaban kowace irin jami’yya ce kuma da shi ne ake samun nasara” inji shi.

Sabon shugaban jam’iyyar PDP ya ce don Allah a manta da duk wani rashin fahimta da ya faru ko yake faruwa a cikin jam’iyyar a matakin jihar Katsina, abinda kawai ya rage masu shine su tunkari yakin neman zaɓe.

Kazalika ya bayyana cewa kofa a buɗe take ga duk wani ɗan jami’yya da ke son bada shawara a kowane mataki, sannan ya yi kira ga ‘ya’yan jami’yyar da su san ya kishin jami’yyar PDP domin a cewar sa ita ke da nasara.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

An Gabatar Da Bidiyon Musamman Na Bayanin Magabata Da Shugaba Xi Jinping Yake So Game Da Yadda Sin Ta Kama Sabuwar Hanyar Neman Samun Ci Gaba

Next Post

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Noma A Matsayin Dan Takarar PDP A Kebbi

Related

Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye
Siyasa

Dalilin Gwamnatin Kano Na Haramta Shirye-shiryen Siyasa Kai Tsaye

2 days ago
Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi
Siyasa

Gwamna Fintiri Ba Zai Bar PDP Ba – Humwashi

5 days ago
Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Wa Da Bappa Bichi Martani
Siyasa

Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Wa Da Bappa Bichi Martani

5 days ago
Atiku Ne Rikitacce Ba Tinubu Ba
Labarai

Atiku Ne Rikitacce Ba Tinubu Ba

1 week ago
Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ki Halartar Bikin Ranar Ma’aikata, Ana Zargin Akwai Takun Saka
Siyasa

Mataimakin Gwamnan Neja Ya Ki Halartar Bikin Ranar Ma’aikata, Ana Zargin Akwai Takun Saka

1 week ago
‘Yan Siyasa Na Komawa APC Don Buƙatar Kansu, Ba Don Jama’a Ba – Dalung
Siyasa

‘Yan Siyasa Na Komawa APC Don Buƙatar Kansu, Ba Don Jama’a Ba – Dalung

1 week ago
Next Post
Babban Kwamatin Ayyuka Na Jam’iyyar PDP Na kasa Ya Gana Da ‘Yan Takarar Gwamna Na Jam’iyyar

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Noma A Matsayin Dan Takarar PDP A Kebbi

LABARAI MASU NASABA

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

Likitocin Sin Sun Ba Da Jinya Kyauta A Yankunan Karkara Na Saliyo

May 9, 2025
Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

Babban Bankin Sin Zai Inganta Hidimomin Kudi Don Habaka Amfani Da Shi

May 9, 2025
Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

Sin Da Rasha Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Zurfafa Dangantakar Abokantaka Ta Hadin Gwiwa Bisa Manyan Tsare-tsare A Sabon Zamani

May 9, 2025
Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

Hukumar Fina-Finai Ta Kasar Sin Ta Kulla Takardar Hada Hannu Da Hukumar Al’adu Ta Kasar Rasha

May 9, 2025
Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

Haraji: Amurka Ta Kama Hanyar Durkusar Da Kanta

May 9, 2025
Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

Kotu Ta Ɗage Shari’ar Yahaya Bello Zuwa 26 Ga Yuni Don Yanke Hukunci

May 9, 2025
Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

Masana Sun Bayyana Ingancin TELA Maize Ga Rayuwar Al’umma

May 9, 2025
Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

Hada-hadar Cinikayyar Waje Ta Kasar Sin Ta Karu Da Kaso 5.6 Bisa Dari A Watan Afirilu

May 9, 2025
Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

Hukumar Raya Arewa Maso Yamma Ta Soke Shirin Tallafin Karatun Ƙasashen Waje

May 9, 2025
GORON JUMA’A 09/05/2025

GORON JUMA’A 09/05/2025

May 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.