Game da matakin Amurka na kakaba “harajin fito na ramuwar gayya”, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya yi bayani a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Amurka ta kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokan cinikayya daga bangare daya, lamarin da ya kwace ‘yancin samun ci gaba na sauran kasashen duniya, musamman kasashe masu tasowa.
Kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya a kwanakin baya, wadanda suka hada da kasashe da yankuna fiye da 180 a duniya, ciki har da wasu kananan kasashe da MDD ta ayyana a matsayin mafi rashin samun ci gaba.
- Matakin Sin Na Karfafa Takaita Fitar Da Abubuwa Masu Alaka Da Ma’adanan “Rare Rarth” Na Nuni Ga Aniyarta Ta Kare Tsaron Kasa
- Sau Biyu Ake Yin Girbin Aya A Shekara – RMRDC
Lin Jian ya bayyana game da wannan batu cewa, kasar Amurka ta yi amfani da dalilin tabbatar da adalci don aiwatar da manufarta ta kama karya, da samun moriya ta hanyar lalata moriyar sauran kasashe, da sanya kanta gaba da komai ba tare da yin la’akari da ka’idojin kasa da kasa ba, yana mai cewa, wannan mataki ne da aka dauka bisa ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya da cin zarafin tattalin arziki.
Hakazalika, Lin Jian ya jaddada cewa, ya kamata kasa da kasa su bi ka’idojin yin shawarwari da samun ci gaba da more fasahohi da juna, da kiyaye bin ra’ayin bangarori daban daban, da kin amincewa da ra’ayin bangare daya da ba da kariya ga cinikayya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa tushen MDD da kuma tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban daban bisa tushen WTO. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp