Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ajandar mulkin duniya a taron “SCO+” na birnin Tianjin a jiya Litinin, kasa da kasa sun mai da hankali sosai ga wannan batu.
Ajandar, wadda shugaba Xi ya fitar ta kunshi wasu ka’idoji guda biyar, wato tabbatar da daidaiton ikon mulkin kasa, da bin dokokin kasa da kasa, da aiwatar da ra’ayin bangarori daban-daban, da ba da shawarar kula da bukatun jama’a, da kuma mai da hankali kan aiwatar da matakai na samar da wata hanya a fayyace ga kasashen duniya wajen gudanar da ayyuka cikin adalci. Wannan ya shaida cewa, ka’idojin biyar suna shafar tushe, da tabbaci, da hanya, da daraja da kuma muhimman ka’idojin mulkin duniya, wadanda suke daidai da ka’idojin kundin tsarin mulkin MDD, da bin begen yawancin kasashen duniya. Alal misali, ajandar ta jaddada cewa, “Akwai bukatar inganta wakilci da murya tsakanin kasashe masu tasowa,” da shawarar “Kauracewa kakaba ‘dokokin gida’ na wasu kasashe a kan sauran kasashe”, da “nuna rashin amincewa da ra’ayin bangare guda daya” da sauran ra’ayoyi suna nufin yanayin rashin adalci da daidaito kan tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya, da kuma samar da hanyar daidaita matsalolin.
Gabatar da ajandar mulkin duniya ya shaida cewa, Sin ta sa kaimi ga kyautata tsarin mulkin duniya bisa yanayin da ake ciki, da samar da hanya ga dan Adam wajen tinkarar kalubale da shimfida duniya mai zaman lafiya da wadata. A halin yanzu, Sin ta kara samar da gudummawarta wajen daukar alhakinta a matsayin babbar kasa a duniya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp