A yau Laraba, sabuwar dokar dake da nufin kare al’adun gargajiya da gine-gine a tsohon garin birnin Kashagar na jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, dake arewa maso yammacin kasar Sin ta fara aiki.
Dokar wadda aka zartar da ita a ranar 31 ga watan Maris, ta haramta rushewa ko lalata gine-gine masu tarihi a tsohon garin, tare da tanadin wajibcin neman izini a hukumance kafin sake fasalin gine-gine.
- Sin Ta Bayyana Adawa Da Matakin Amurka Na Amincewa Da Kuduri Mai Kunshe Da Matakai Marasa Kyau Game Da Sin
- An Yi Gwajin Tafiya Cikin Teku Na Jirgin Ruwa Mai Dauke Da Jiragen Saman Yaki Na Uku Na Sin
Haka kuma, ta ce dole ne a kare al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba kamar fasahohin gargajiya da tatsuniyoyi da bukuwa, da kaucewa neman samun ribar da ta wuce kima daga gare su.
Bugu da kari, dokar tana karfafawa al’ummomin tsohon garin daga mabambantan kabilu gwiwar zama cikin gidajensu na asali tare da taimakawa kokarin da ake na kare tsohon garin. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)