Wasu shekaru 51 da suka wuce, wato a ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 1971, aka zartas da wani kuduri a babban taron Majalisar Dinkin Duniya (MDD), inda aka maido da kujerar jamhuriyar jama’ar kasar Sin (sabuwar kasar Sin) a majalisar.
Wani bidiyon da aka dauka a lokacin ya nuna yadda wasu jami’an kasashen Afirka da suka halarci taron MDD suka yi matukar murnar ganin yadda sabuwar kasar Sin ta samu wannan nasara.
Tsohon shugaban kasar Sin Mao Zedong ya taba bayyana cewa, ‘yan uwa na nahiyar Afirka sun dauki sabuwar kasar Sin, sun kai ta cikin MDD.
Hakika cikin kasashe 23 da suka gabatar da bukatar shigar da sabuwar kasar Sin cikin MDD, fiye da rabinsu kasashe ne daga nahiyar Afirka.
Sa’an nan, a lokacin da aka jefa kuri’a kan batun a majalisar, an jefa kuri’un amincewa 76, inda kuri’u 26, ko kuma mu ce kashi 1 bisa kashi 3 daga cikinsu, kuri’u ne da kasashen Afirka suka jefa.
Amma mene ne dalilin da ya sa kasashen Afirka suka nuna goyon baya ga sabuwar kasar Sin don ganin komawarta cikin MDD?
Shi ne domin a lokacin, ko da yake sabuwar ba a maido da kujerar kasar Sin cikin MDD ba tukuna, sakamakon yunkurin kasar Amurka na hana ruwa gudu game da batun, duk da haka, sabuwar kasar Sin ta yi kokarin kare adalci a duniya, inda kasar ta gabatar da ka’idoji biyar na zama tare cikin sulhu, da gina layin dogon da ya hada Tanzania da Zambia kyauta, da ba da taimako ga dimbin kasashen dake nahiyoyin Afirka, da Asia, da Latin Amurka, a fannin yakar ‘yan mulkin mallaka, da neman ‘yancin kansu.
Zuwa yanzu, wasu shekaru 51 sun shude. Idan aka waiwayi baya, ko zabin da kasashen Afirka suka yi ya yi daidai?
Za a tuna da cewa, cikin shekaru 51 da suka wuce, kasar Sin ta halarci kusan dukkan kungiyoyin kasa da kasa na tsakanin gwamnatoci, da sa hannu kan yarjeniyoyin kasa da kasa fiye da 600. Kana kasar ta zama ta biyu a fannin yawan samar da kudi ga MDD. Haka zalika, ta tura sojoji fiye da dubu 50, don gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a wurare daban daban na duniya.
Ba za a manta da yadda kasar Sin ta samar da gudunmowa ga aikin daidaita kundin tsarin MDD don tabbatar wa kasashe masu tasowa damar tura wakilansu don zama babban sakataren majalisar ba. Abin da ya daukaka matsayin kasashe masu tasowa, da ba su karin ikon fada a ji.
Sa’an nan a taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin mai rike da ragamar mulki a kasar, Xi Jinping, babban magatakardan jam’iyyar, kana shugaban kasar Sin, ya nanata babbar manufar kasar Sin ta kare zaman lafiya a duniya, da baiwa kasashe daban daban damar samun ci gaba tare.
Hakan ma ya shaida muhimmiyar rawar da kasar Sin ke takawa a duniya, inda take kokarin neman ganin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Vernon Mwanga, wani tsohon jami’in diplomasiya ne na kasar zambia, wanda ya taba jefa kuri’ar amincewa don taimakawa kasar Sin komawa cikin MDD. Yanzu, da ya waiwayi aikin da ya yi a lokacin, ya gaya ma ‘yan jaridu cewa, “wannan abun alfahari ne mafi muhimmanci da na taba yi a duk tsawon rayuwata”. (Bello Wang)