Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya jaddada bukatar samar da dorewar zaman lafiya da hadin kai a jihar da ma Nijeriya baki daya, domin samun ci gaban kasa mai dorewa.
Gwamna wanda kuma shi ne Shugaban kungiyar gwamnonin APC a Nijeriya, ya yi wannan kiran a sakonsa na sabuwar shekara ga al’umar jihar.
- Gyaran Kundin Tsarin Mulki Ne Zai Hana Cin Kudin Kananan Hukumomi – Bagudu
- Bagudu Ya Fitar Da Naira Miliyan 30 Don Daukar Nauyin ‘Yan Wasan Kebbi
Bagudu ya ce, zaman lafiya da hadin kai su ne ababe biyu mafiya muhimmanci wajen kawo ci gaban kasa.
Jihar Kebbi tana cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Nijeriya sakamakon yadda al’umar jihar suka nuna amincewa da zaman lafiya da son ci gaban kasa baki daya.
Gwamnan ya yi kira ga al’umar kasar da su kasance masu kishin kasa da kaunar juna.