Kungiyar Fityanul Islam a Nijeriya, ta nuna adawarta dangane da ce-ce-ku-ce kan yarjejeniyar Samoa da ake zargin Nijeriya da sanya hannu a kai domin samun rancen dala biliyan 150. Kungiyar ta nemi mambominta da su fito su gudanar da zanga-zangar kin amincewa da yarjejeniyar.
Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Muhammad Arabi AbulFathi, shi ne ya shaida hakan a cikin sakonsa na sabuwar shekarar Musulunci na 1446 da ya fitar a Abuja.
- Matsalar Tsaro: Gwamnatin Zamfara Ta Sanya Dokar Takaita Zirga-zirgar Ababen Hawa
- An Kaddamar Da Cibiyar Nuna Hadin Gwiwar Sin, Afrika Da MDD A Beijing
A cewar kungiyar, a daidai lokacin da ake shiga sabuwar shekarar musulunci, tana kira ga Musulmai baki daya da su ci gaba da gudanar da harkokinsu bisa koyarwar addinin Islama domin wanzar da zaman lafiya, kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
Shugaban ya ce, “Ina kira ga dukkanin mabiyanmu na Tarikar Tijjaniyya da su ci gaba da koyi da rayuwar jagoranmu Sheikh Ahmad Tijjani (RTA), Sheikh Ibrahim Nyass (RTA), wanda suka nuna mana tsantsan yadda ake son Manzon Allah, An-nabi Muhammad (SAW).”
A wata sanarwa mai dauke da sanya hannun kakakin kungiyar, Ustaz Sani Ibn Sa-lihu, kungiyar ta yi kira ga Musulmai da su yi amfani da ranar goma ta farko na watan Muharram wajen yin azumi da addu’ar neman taimakon Allah kan matsatsin tattalin arziki, siyasa, matsalolin tsaro da dukkanin kalubalen da ke ad-dabar Nijeriya, domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen wadannan matsalolin.
“Muna da mambobi sama da miliyan 50 na Tarikar Tijjaniyya, ‘yan kungiyar Fit-yanul Islam a Nigeria, ina kira a gareku da ku ci gaba da goyon bayan kungiyar, sannan ina kira ga dukkanin rassanmu da suke kananan hukumomi 774 a jihohi 36 cikin har da Abuja da su dauki zancen rajistan mambobi da muhimmanci.”
Sheikh Arabi ya gode wa hukumomin da suke taimakon kungiyar, musamman gwamnatin Kaduna da Katsina da kuma jinjina wa irin kyawawan dabi’un mam-bobinsu.