Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa jihar Kebbi bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu na ganawa da Gwamnatin Jihar da iyalan ‘yan matan makarantar da aka sace daga Makarantar sakandare ta Gwamnati, Maga, Karamar Hukumar Danko-Wasagu Ta Jihar.
Mataimakin Shugaban Kasa zai gana da Gwamna Nasiru Idris, Sarakuna, Shugabannin tsaro, da iyayen yaran Da Aka Sace.
ADVERTISEMENT
Shugaba Tinubu ya umarci Mataimakin Shugaban Kasa da ya tabbatar wa jama’ar Jihar Kebbi cewa, Gwamnatin Tarayya za ta tabbatar da an kuɓutar da ‘Yan matan da ska sace cikin sauri kuma cikin koshin lafiya.














