• English
  • Business News
Sunday, August 10, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sahihanci Ya Sa Kasar Sin Samun Karbuwa A Nahiyar Afirka

by CGTN Hausa
1 year ago
in Ra'ayi Riga
0
Sahihanci Ya Sa Kasar Sin Samun Karbuwa A Nahiyar Afirka
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shahararren kamfanin tantance ra’ayin jama’a na Gallup, ya gabatar da wani sakamakon binciken da ya yi a kwanan baya, inda ya ce kasar Sin ta zarce kasar Amurka, ta zama wadda ta fi tasiri a nahiyar Afirka. Alkaluman da kamfanin ya gabatar sun nuna cewa, ‘yan Afirka da suke goyon bayan kasar Sin, sun karu daga kashi 52% a shekarar 2022, zuwa kashi 58% a shekarar 2023. Yayin da a daya bangaren, masu goyon bayan kasar Amurka suka ragu daga kashi 59% a shekarar 2022, zuwa kashi 56% a bara.

Wannan sakamakon bincike ya yi daidai da sakamakon nazari da wasu hukumomin binciken ra’ayin jama’a na kasashen Afirka, irinsu Afrobarometer mai hedkwata a kasar Ghana, da Ichikowitz Family Foundation dake kasar Afirka ta Kudu, suka gabatar, inda dukkansu suka sanya kasar Sin a gaban kasar Amurka, a fannin samun karbuwa.

  • An Gudanar Da Bikin Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Serbia A Belgrade
  • Matsayar Sin Da Faransa Ta Bayyana Lamirin Bil Adama Na Kare Adalci

Sai dai me ya sa masu goyon bayan kasar Amurka suka ragu? Kamfanin Gallup bai yi wani karin bayani ba. Amma a ganina a kalla akwai dalilai 2.

Na farko, kasar ta kan keta adalci a al’amuran duniya. Misali, a rikicin Falasdinu da Isra’aila na wannan karo, kasar Amurka ta yi ta samar da tallafin makamai ga Isra’ila, abin da ya haddasa dorewar rikicin, gami da tsanantar matsalar jin kai, lamarin da ya janyo dimbin suka daga gamayyar kasa da kasa.

Na biyu, yadda kasar ke kallon kanta kamar “baba”, da son tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe. Misali, a nahiyar Afirka, kasar Amurka ta nemi hana kasar Uganda zartas da dokar haramta luwadi, da hana kasar Niger kulla hulda da Rasha da Iran, da dai sauransu.

Labarai Masu Nasaba

Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu

Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?

Sa’an nan a daya bangaren, dalilin da ya sa kasar Sin kara samun karbuwa a nahiyar Afirka, shi ne yadda ta magance kurakuran da Amurka ta tabka. A cewar wani shehun malami mai suna Adhere Cavince na kasar Kenya, manufar diplomasiyya ta kasar Sin ta jaddada muhimmancin girmama ikon mulkin kai na sauran kasashe, da rashin tsoma baki cikin harkokin gidansu, da kallon kanta a matsayin kawa maimakon babbar kasar dake da karfi. Wadannan manufofi na kasar Sin sun burge kasashen Afirka, wadanda suka dade suna shan wahalar mulkin mallaka, da shisshigin da kasashen yamma suke yi musu.

Cikin wani bayani mai taken ” Me ya sa kasar Sin ta fi kasar Amurka samun karbuwa a nahiyar Afirka?” da Mista Cavince ya rubuta, wanda aka buga cikin jaridar the Nation ta kasar Kenya, ya ce, kasar Sin na dora muhimmanci kan hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki, ba tare da gindaya sharadi na siyasa ba, sabanin abun da kasar Amurka ta kan yi, na alakanta tallafi da zuba jari da sharuda na siyasa, irinsu batun hakkin dan Adam, da tsarin da ake bi wajen gudanar da mulki. Ta wannan hanya, kasar Sin ta samar da dimbin damammaki ga kasashen Afirka, na kiyaye tsarinsu na siyasa, gami da neman dabarar raya tattalin arziki, a lokaci guda.

Ban da haka, Mista Cavince ya ambaci hakikanin ci gaban da kasar Sin ta haifar wa nahiyar Afirka. Inda hadin gwiwar “Ziri Daya da Hanya Daya” ya inganta kayayyakin more rayuwa na kasashen Afirka, da ba da damar raya tattalin arziki, da dunkulewar kasashen Afirka waje guda. Kana zuba jari da kasar Sin take yi ya zama muhimmiyar damar samun kudin shiga da guraben aikin yi ga kasashen Afirka. Haka zalika, yadda kasar Sin ke samar da kudin tallafin karatu ga daliban Afirka domin su yi karatu a kasar Sin, ya karfafa cudanya tsakanin al’ummun bangarorin 2, da ba matasan kasashen Afirka damar kara fahimtar kasar Sin. Sa’an nan ta hanyar raba nagartattun fasahohinta, kasar Sin ta zame wa kasashen Afirka muhimmiyar kawar hadin kai, a kokarinsu na neman ci gaban kasa.

Hakika ainihin dalilin da ya sanya kasar Sin daukar wadannan matakai shi ne tunanin kasar na musamman a fannin hadin gwiwa da kasashen Afirka, wato gaskiya, da kauna, da sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako. Idan wata kasa, yayin da take hulda da sauran kasashe, ta iya nuna wani yanayi na daidaito, da rashin yaudara ta akidar siyasa, da kokarin cika alkawarin da ta dauka, da samar da hakikanin alfanu ga sauran kasashe, ta hanyar hadin gwiwar ta moriyar juna, to, ba za a ki kaunarta ba. Saboda haka, za mu iya cewa, wannan ra’ayi na nuna sahihanci, da samar da hakikanin sakamako na kasar Sin, shi ne tushen hulda mai kyau dake tsakaninta da kasashen Afirka.

Bisa haka, za mu iya hasashen cewa, bayan kasar Sin da kasashen Afirka sun kara karfafa hadin kansu na amfanawa juna a kai a kai, huldar dake tsakaninsu ma za ta kara kyautatuwa. (Bello Wang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: AmurkaCGTNFaransa
ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Ɗumi-ɗumi: EFCC Za Ta Gurfanar Da Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama Da ‘Yarsa A Gobe Alhamis

Next Post

Shugaba Xi Ya Sanar Da Matakai 6 Da Za Su Tallafa Wajen Gina Alumma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Sin Da Serbia

Related

Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
Ra'ayi Riga

Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu

2 days ago
Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?
Ra'ayi Riga

Ta Yaya Za a Ba Matasa Damar Raya Kansu?

3 days ago
Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe
Ra'ayi Riga

Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe

6 days ago
Amurka: “Afirka Ba Ta Cikin Jerin Fannoni Da Muka Ba Da Fifiko A Kai”
Ra'ayi Riga

Amurka: “Afirka Ba Ta Cikin Jerin Fannoni Da Muka Ba Da Fifiko A Kai”

1 week ago
Mai Cin Moriyar Kai Da Mai Cin Moriyar Juna
Ra'ayi Riga

Mai Cin Moriyar Kai Da Mai Cin Moriyar Juna

2 weeks ago
Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!
Ra'ayi Riga

Bai Kamata a Rika Kai wa Fararen Hula Hari Ba!

3 weeks ago
Next Post
Shugaba Xi Ya Sanar Da Matakai 6 Da Za Su Tallafa Wajen Gina Alumma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Sin Da Serbia

Shugaba Xi Ya Sanar Da Matakai 6 Da Za Su Tallafa Wajen Gina Alumma Mai Makoma Ta Bai Daya Ga Sin Da Serbia

LABARAI MASU NASABA

Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho

Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho

August 10, 2025
Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata

Jihar Kogi Ta Kafa Kotuna 9 Don Hukunta Masu Cin Zarafin Mata

August 10, 2025
NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja

NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja

August 10, 2025
Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa

August 10, 2025
Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 

Nazari Kan Dalilin Da Ya Sa Kajin Gidan Gona Ke Samar Da Ƙananan Ƙwai 

August 10, 2025
Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya

Abubuwan Da Suka Ja Hankalin Gwamnatin Tarayya Ta Ƙaddamar Da Tsarin Noman Waken Soya

August 9, 2025
Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

Philippines Za Ta Girbi Sakamakon Rura Wutar Rikici Kan Taiwan

August 9, 2025
Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027

August 9, 2025
Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar

August 9, 2025
Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10

Sanatocin Da Ba Su Kawo Ƙudiri Ba Tun Bayan Ƙaddamar Da Majalisar Dattawa Ta 10

August 9, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.