Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin shirin namu na ado da kwalliya.
Abubuwan da Uwargida za ta tanada:
Ganyan Gwanda, Ganyan Ayaba, Ganyan Lalle ko lallan idan ba a su ganyan ba , Ganyan magarya:
Wannan hadi yanada kyau so sai musamman ga fatar fuska sannan kuma yana gyara fuska ta yi laushi, ta yi sheki, ta yi luwe-luwe, tayi santsi ta yi gyalli kamar ruwa ba zai tsaya ba sai kin gwada Uwargida zaki gane abin da nake nufi, sannan zaki iya amfani da wannan hadi duk jikin ki.
Da farko zaki samu wadannan ganyayyaki da muka ambata sai ki hadesu waje daya sannan ki nikesu ko ki daka su duk de wanda yafi miki sauki su yi laushi idan zakiyi amfani dashi sai kidan samasa ruwa ki kwaba sannan kuma zaki iya kwabashi da madara ta ruwa duk de wanda kikayi duk dayane za ki iya samun danya su lokacin da zaki yi amfani da shi sai ki kirbashi sai ki shafa a fuskarki kibarshi ya yi kamar minti goma sha biyar haka sannan ki samu tushu ko wani gyalle haka wamda zai goge miki sai ki gogeshi in sha Allahu zaki ga yadda fuskarki za ta yi da izinin Allah.