Jigo a haɗakar jam’iyyar ADC, Salihu Mohammed Lukman, ya ce dole ne sai jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar nan sun haɗa kansu a waje ɗaya, sannan za su iya tunkarar jam’iyyar APC zaɓen 2027.
Lukman ya bayyana haka ne a Kaduna, a wata tattanawa da ya yi da ‘yan jarida, inda wasu shugabannin jami’iyyu da sauran masu ruwa da tsaki da suka fito daga jihar suka halarci taron tattaunawar.
- Yawancin ‘Yan Siyasar Nijeriya Ba Su Da Tarbiyya – Sarki Sanusi II
- SDP: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Wa El-Rufai Shaguɓe Da Ayyana Shi A Matsayin Ɗan Gudun Hijirar Siyasa
Ya ce, “Domin a cimma hakan ne ya sanya muka yanke shawarar zuwa ga jiga-jigan ‘yan siyasa a ƙasar domin mu tattauna da su, mu kuma janyo ra’ayoyinsu domin su amaince mu yi aki tare wajen samun nasara kan APC tun daga matakin ƙasa har zuwa na jihohi a zaɓukan 2027, ” Inji Luluman.
Ya kuma yi kira ga ‘ya’yan jami’yyar ADC da su haɗa kai waje ɗaya tare da kawar da duk wani son rai a tsakaninsu ta yadda za su iya tunkari zaɓukan da ke tafe a 2027.
Ya sanar da cewa, sun cimma matsayar su ɗauki ADC a matsayin wata hanya da za su yi gamayyar bisa yarjejeniya da fahimtar juna kan yi wa ADC garanbawul, musamman a ƙidojinta.
A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya.
Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC, ya koka kan yadda gwamnatin Kaduna ba ta kula da haƙƙoƙin ma’aikatan jihar da rashin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu da ƙalubalen rashin tsaro wanda hakan ke hana manoma zuwa gonakansu.
Ya soki tsarin rabar da takin zamani na gwamnatin jihar ke gudanarwa ba tare da ta magance ƙalubalen rashin tsaro ba daga tushe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp